Tsirarun hotunan Aisha Buhari guda 9 da ya kamata ku gani
An haifi Aisha Buhari, Uwargidan shugaban kasa Muhammadu Buhari a ranar 17 ga watan Fabrairu, 1971. Kyakkyawar matar shugaban Najeriya kuma mai aji ta cika shekara 46 a yau.
An haifi Aisha Buhari a jihar Adamawa inda a nan tayi makarantar Firamare da sakandare. Tana zaune da kanenta da yan’uwanta. Matar shugaban kasar ta fito daga tushe mai karfi kamar yadda kakanta ya kasance ministan tsaro na farko a Najeriya.
Mahaifinta ya kasance injiniya yayinda mahaifiyarta ta fito daga ahlin gidan manoma da rinin kaya.
Ta auri shugaban kasa Muhammadu Buhari wanda a lokacin yana da yara biyar daga matarsa ta farko a 1989. Yan Najeriya sun sa Aisha Buhari a matsayin matar shugaban kasa, gwana a gurin kwaliyya, kyakkyawa kuma marubuciya.
Hotunan Aisha a wannan rubutu ya nuna ta a haske na daban. Wadannan hotunan sun karkata ga bangaren na daban a rayuwarta; za’a ganta a matsayin Uwa, kyakkyawa, mace mai manufa sannan kuma mai bada goyon baya a duk wani abu da zai inganta al’umma.
Kalli tsiraru kuma kyawawan hotunan Aisha Buhari a kasa:
1 .A matsayin matar mutun mafi karfi a Najeriya
2 .Aisha Buhari mace ce mai son jama’a
3. Mace mai son addinin musulunci
5. Ta kasance uwa ta gari mai kyau
6. Babu shakka uwargidan shugaban kasa mace ce mai son ado
7. Aisha Buhari tare da Michelle Obama
8. Aisha da shugaban kasa cikin kauna a shekarun baya
9. Uwa mai kaunar yayanta
Asali: Legit.ng