YANZU-YANZU: An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Katsina
1 - tsawon mintuna
Labarin da ke iso mana yanzu yana nuni da cewa an tsige kakakin majalisar dokokin jihar Katsina RT Hon. Aliyu Sabi'u Muduru da safiyar yau.
Tuni dai har sauran yan majalisar sun zabi Honarable Yahaya Kusada don ya maye gurbin sa.
Bayanan da muka samu ikon tattarowa suna nuni da cewa yan majalisu 23 cikin 34 suka rattaba hannu kan amincewa da hakan.
Mai karatu dai zai iya tuna cewa Hon. Aliyu Sabi'u Muduru yayi zama wanda yafi kowa zama mai karancin shekaru a lokacin da ya zama kakakin majalisar dokokin jihar ta Katsina.
Asali: Legit.ng