Sunan Allah ya bayyana a jikin Akuya (HOTO)

Sunan Allah ya bayyana a jikin Akuya (HOTO)

An gano hoton wani akuya wanda ke dauke da rubutun larabci a jiki

A cewar rahoton, Sunan Allah mai girma da na fiyayyen hallita Anabi Muhammad ya bayyana a jikin akuya a kasar Larabawa da ba’a ambata sunan sa ba. An gano zanen ne a lokacin da ake duba akuyan a wani lambu da ake ajiye dabbobi. Da dama sun dauki wananna a matsayin wani babban mu’ujiza!

KU KARANTA KUMA: An kama manyan kwamandojin kungiyar Boko Haram 9 (HOTUNA)

Kalli hoton a kasa:

Sunan Allah ya bayyana a jikin Akuya (HOTO)
Sunan Allah ya bayyana a jikin Akuya

Kwanaki da suka shige ne, aka ga wasu bishiyoyin zogale guda biyu dauke da sunan Allah a jiki. Bayyanan sunan Allah a jikin bishiyoyin zogalen dake gidan wasu Kiristoci ya sa unguwarsu ya zamo gurin ziyara, inda dubban mutane sukaje addu’a don neman tabbaraki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng