‘Yata da mijina suna da wata alaka, kuma bazan iya dakatar da shi ba – wata mata ta koka

‘Yata da mijina suna da wata alaka, kuma bazan iya dakatar da shi ba – wata mata ta koka

- Wata mata daga amurka ta gano cewa mijinta da yarta na da wani alaka

- Matar ta tunkare su amma sun karyata ta

- Mijin matar ba shine mahaifin yarinyar ba

- Tsoron matar shine cewan idan ta bar mijinta zata rasa gidan ta

- Mahaifiyar yarinyar na neman shawara daga Ravishly’s advice columnist Erin

‘Yata da mijina suna da wata alaka, kuma bazan iya dakatar da shi ba – wata mata ta koka
Matar tace ta shiga rudani

Wata mata da ba’a bayyana ba daga Amurka ta gano cewa babban yarta da mijinta suna da wani alaka amma da ta tunkare su sun karyata cewa babu wani abu a tsakaninsu.

Mahaifiyar yarinyar ta aika sako ga Ravishly’s Ask Erin advice game da abunda ke faruwa, kuma tace bazata iya jure ma haka ba. Sakon ya bayyana yadda ta tunkari abokin zaman nata da ‘yarta kuma ta bayyana yadda take ji game da al’amarin wanda acewar ta gaskiya ne duk da sun karyata hakan.

KU KARANTA KUMA: An kama wasu yan mata biyu suna sumbatar junansu a bainar jama’a (hoto)

Ta rubuta: “Tun lokacin, na sha kamasu suna musayar sakonni tsakaninsu, suna bayyana yadda suke kaunar junansu. Na kuma samu katin soyayya da suke ba junansu. Bazan iya jure ma haka ba; matar ta rubuta. Bazasu daina ban i kuma abun na damuna da yi mun radadi a zuciyata."

Matar ta kuma bayyana cewa mijin nata ba shine uban yarinyar ta da yake aikata masha’a da it aba, kuma cewa ta dogara da shine ta fannin kudi, don haka tana tsoron barin sa domin tana iya rasa gidanta da duk wani abu da ta rasa.

Shawarar da Erin suka bata shine cewan aikwai bukatar ta bar mijin nata saboda yanzu ne lokacin da zata kula da kanta.

Asali: Legit.ng

Online view pixel