Buhari ya tarbi sarkin Morocco
1 - tsawon mintuna
Shugaban kasa Muhammadu Buhari yana ganawa tare da sarki Mohammed VI na Morocco a fadar shugaban kasa dake Abuja.
Sarki Mohammed VI na Morocco ya isa ofishin shugaban kasa da misalign karfe daya da rabi (1:30) daidai inda ya samu tarba daga shugaban kasa Muhammadu Buhari da wasu manyan jami’an gwamnati.
Mataimakin Shugaban kasa Farfesa Yemi Osinbanjo ya tarbi sarki Mohammed VI na Morocco a daren ranar Alhamis a Abuja lokacin da ya iso kasar.
KU KARANTA KUMA: Masu Magana da yaren Hausa sun kai miliyan 120 a Najeriya
Ga wasu hotunan a kasa:
Asali: Legit.ng
Tags: