'Yar Sandan Najeriya Ta Kafa Tarihi, Ta Doke Kasashe a Gasar Duniya

'Yar Sandan Najeriya Ta Kafa Tarihi, Ta Doke Kasashe a Gasar Duniya

  • 'Yar sandan Najeriya, Juliet Chukwu ta lashe kambun Bantamweight a gasar dambe ta EFC119 da aka yi a birnin Johannesburg
  • Sufeto Janar na ‘yan sanda, Kayode Adeolu Egbetokun, ya yaba da nasarar yana mai tabbatar da cigaba da goyon bayan harkar wasanni
  • Nasarar Juliet Chukwu ta biyo bayan ƙaddamar da kafa ƙungiyar MMA ta ‘yan sandan Najeriya domin inganta wasanni a fadin kasar nan

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja, Nigeria - Rundunar ‘yan sandan Najeriya ƙarƙashin jagorancin Sufeto Janar, Kayode Adeolu Egbetokun ta samu wata babbar nasara a fannin wasanni.

Jami'ar 'yan sanda, Juliet Chukwu ta lashe kambun Bantamweight a gasar damben EFC119 da aka yi a birnin Johannesburg a Afrika Ta Kudu.

Kara karanta wannan

Sojoji sun durfafi 'yan ta'addan Lakurawa, sun samu tarin nasrori

Najeriya
Yar sandan Najeriya ta lashe gasa a duniya. Hoto: Nigerian police Force
Asali: Facebook

Rundunar 'yan sanda ta wallafa a Facebook cewa nasarar fito da ƙwarewar ‘yan wasan Najeriya a idon duniya, tare da ƙarfafa alƙawarin rundunar na inganta wasanni a dukkan fannoni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sufeto Janar na ‘yan sanda ya ce nasarar wata alama ce ta ƙudurin rundunar wajen ganin ta tallafa wa ma’aikata a dukkan fannoni, musamman fannin wasanni.

Sufeto Janar ya yabawa Juliet Chukwu

Channels Television ya rahoto cewa IGP Egbetokun ya tabbatar da cewa rundunar za ta ci gaba da tallafa wa Juliet Chukwu da sauran ma’aikatan da suka nuna ƙwarewa a fannin wasanni.

"Rundunar ‘yan sanda ta yi fice a fannoni da dama, daga samun nasarori wajen rage laifuffuka har zuwa kyautatawa a fannin wasanni.
Wannan nasara tana daga cikin jerin ci gaban da muka samu a bana."

- Sufeto Janar Egbetokun

Za a cigaba da goyon bayan 'yan sanda

Kara karanta wannan

An kama rikakken 'dan bindiga mai raba makamai a jihohin Arewa

Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da cewa tana da shirin ci gaba da aiwatar da ayyuka da tsare-tsare domin samun nasara a fannoni daban-daban, ciki har da wasanni.

Kakakin rundunar, ACP Olumuyiwa Adejobi ya ce ƙoƙarin na cikin manufofin rundunar na haɓaka kwarewa da kuma samar da yanayi mai kyau ga ma’aikata domin yin fice a ayyukansu.

'Yan sanda sun kama ma'aikacin banki

A wani rahoton, kun ji cewa rundunar ƴan sandan jihar Katsina ta cafke wani ma'aikacin banki bisa zarginsa da satar kuɗin abokan hulda.

An ruwaito cewa jami'an ƴan sandan sun cafke wanda ake zargin ne bayan wani abokin huld ya shigar da ƙorafi a kan satar da aka masa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng