Amorim: Sabon Kocin Manchester United Ya Kama Aiki, An Sallami Mutum 4 daga Kulob

Amorim: Sabon Kocin Manchester United Ya Kama Aiki, An Sallami Mutum 4 daga Kulob

  • Sabon kocin da Manchester United ta ɗauka daga kungiyar Sporting Lisbon, Ruben Amorim ya isa Carrington gabanin fara aiki
  • Kungiyar kwallon kafar ce ta tabbatar da haka a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, ta ce Amorim ya samu kyakkyawar tarba
  • Man United ta kuma tabbatar da tafiyar Ruud Van Nistelrooy da ƴan tawagarsa mutum uku bayan gama aikin wucin gadi da aka ba su

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Manchester, UK - Sabon kocin Manchester United, Ruben Amorim ya samu kyakkyawar tarba yayin da ya isa kungiyar yau Litinin, 11 ga watan Nuwamba.

Amorim ya karɓi aikin horar da ƙungiyar ne bayan korar Erik Ten Hag, wanda al'amuran Man United suka fara taɓarɓarewa a karkashinsa.

Ruben Amorim.
Ruben Amorim ya dura a Manchester United Hoto: Manchester United
Asali: Facebook

Kungiyar kwallon kafa ta Manchester United ta tabbatar da isowar sabon kocin a wata sanarwa da ta wallafa a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Ta faru ta kare, gwamnati ta sanya ranar cefanar da kadarorin babban banki

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Amorim ya isa Manchester United

Shugaban sashen gudanarwa na Manchester United, Omar Berrada shi ne ya tarbi sabon kocin tare da tawagarsa.

Sanarwar ta ce:

"Shugaban gudanarwa, Omar Berrada ya tarbi Ruben Amorim da runguma a kofar shiga sashen ƴan wasa.
"Daraktan harkokin wasanni, Dan Ashworth da daraktan sashen fasaha Jason Wilcox sun fita wurin tarbar sabon kocin.

Amorim zai gana da manyan ma’aikata a shirye-shiryen fara aiki a matsayin sabon mai horarwa na Man United da zarar an ya samu Visa.

Kociyan dan kasar Portugal mai shekaru 39 ya lashe kofin Primeira Liga biyu da Sporting Lisbon.

Van Nistelrooy ya gama aikin wucin gadi a Man Utd

Kungiyar Manchester United ta kuma tabbatar da cewa Ruud Van Nistelrooy da wasu mutum uku sun bar kungiyar, ta masu fatan alheri a aikinsu na gaba.

Van Nistelrooy ya gama aikin kocin wucin gadi a wasan da Man United ta casa Leicester City ta ci 3-0 ranar Lahadi a filin wasa na Old Trafford.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu zai lula ƙasar waje, zai halarci muhimmin taro da ya shafi Musulunci

Ballon d'Or: Yadda Lookman ya samu maki 82

A wani rahoton, an ji cewa ɗan wasan Najeriya, Ademola Lookman, ya samu maki 82 daga kasashe 17 a nahiyoyi uku a neman lashe kyautar Ballon d’Or.

Tauraron na Atalanta ya samu goyon baya mafi karfi daga kasarsa Najeriya, sai kuma kasar Girka da ta ba shi fifiko a Turai.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262