Super Eagles: Tawagar Ƴan Kwallon Najeriya Ta Dura a Kano, Bayanai Sun Fito

Super Eagles: Tawagar Ƴan Kwallon Najeriya Ta Dura a Kano, Bayanai Sun Fito

  • Manyan ƴan wasan kwallon kafan Najeriya sun dawo gida bayan 'wulaƙanta' su a filin jirgin sama na ƙasar Libya
  • Ƴan wasan sun kwana a filin jirgi da suka je ƙasar domin buga wasan zagaye na biyu na neman gurbi a gasar cin kofin Afirka
  • Hukumar CAF ta kaddamar da bincike kan abin da ya faru da ƴan wasan Najeriya a Libya tsakanin ranakun Lahadi da Litinin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kano - Tawagar ƴan kwallon Najeriya watau Super Eagles ta sauka a filin sauka da tashin jiragen sama na Aminu Kano da ke birnin Kano.

Jirgin da ya ɗauko manyan ƴan kwallon ya sauka a filin jirgin da yammacin yau Litinin, 14 ga watan Oktoba, 2024 daga kasar Libya.

Kara karanta wannan

Mummunar ambaliyar ruwa ta jefa mutane miliyan 2 cikin babbar matsala a Arewa

Yan wasan Najeriya.
Super Eagles ta dawo Najeriya bayan abin da ya faru a Libya Hoto: @supereagles
Asali: Twitter

Daily Trust ta ce ƴan wasan sun tafi Libya ne domin buga zagaye na biyu a wasan neman gurbin shiga gasar cin kofin Afirka amma hakan ba ta yiwu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me ya faru da 'yan Super Eagles a Libya?

Tawagar Super Eagles ta dawo gida Najeriya ba tare da buga wasan ba saboda wulaƙanta ƴan wasan da aka yi a filin jirgin ƙasar Libya.

Rahoton Leadership ya nuna cewa ƴan ƙwallon Najeriya dai sun makale a harabar filin jirgin Libya na tsawon sa'o'i daga ranar Lahadi zuwa safiyar Litinin.

Lamarin ya haifar da ce-ce-ku-ce da sukar Libya, inda daga bisani ƴan wasan Super Eagles suka juyo kai tsaye suka dawo ba tare da buga wasan ba.

CAF ta fara gudanar da bincike

Tuni dai hukumar kwallon ƙafa ta nahiyar Afirka (CAF) ta fara bincike kan abin da ya faru da Super Eagles a filin jirgin saman Libya.

Kara karanta wannan

Soke hukumar EFCC: Gwamna ya saba da takwarorinsa, ya ba da shawara

A wata sanarwa da ta fitar, CAF ta umarci kwamitin ladabtarwa ya gudanar da bincike mai zurfi domin gano abin da ya jawo maƙalewar Super Eagles.

Super Eagles: LFF ta ce kuskure aka samu

A wani labarin kuma hukumar kwallon kafa a kasar Libya ta yi bayani kan makalewar yan kwallon Najeriya a filin jirgin sama.

Hukumar LFF ta musanta zargin cewa ta wahalar da yan kwallon Najeriya ne da gangan yayin da suka je buga wasan neman gurbi.

Muhammad Malumfashi, babban edita a sashen Hausa na Legit ya duba labarin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262