Najeriya 1 vs 2 Cote d'Ivoire: Najeriya Ta Sha Kaye a Hannun Cote d'Ivoire a Wasan Karshe
Tawagar Super Eagle na Najeriya za ta fafata da Elephants na Cote d'Ivoire a wasan karshe na AFCON a katafaren filin Stade Alassane Ouattara, Ebimpe, a ranar Lahadi 11 ga watan Fabrairu.
Za a fara wasan tsakanin manyan kasashen biyu ne karfe 9 lokacin Najeriya. Kungiyoyin biyu sun taba haduwa sau bakwai a AFCON, na karshen Super Eagles ta doke Elephants 1-0 a matakin 'group' na AFCON 2023.
Kasance da Legit Hausa domin samun rahoto kai tsaye kan yadda wasar za ta kaya
Cote d'Ivoire ta lashe kofin AFCON na 2023 bayan doke Najeriya
Tawagar Elephants na Cote d'Ivoire ta doke Super Eagles a wasan karshe na gasar cin kofin nahiyar Afirka (AFCON) da aka yi a kasar ta Cote d'Ivoire. An tashi wasan da 2 - 1 bayan alkalin wasa ya kara mintuna bakwai.
An yi karin mintuna bakwai
An kara mintuna bakwai a wasar karshe tsakanin Najeriya da Cote d'Ivoire a AFCON 2023.
Ivory Coast sun ci kwallonsu na biyu
Elephants na Cote d'Ivoire yanzu sune kan gaba da kwallaye biyu yayin da Super Eagles na Najeriya ke da kwallo daya.
An cire Alex Nwobi
Kocin Najeriya Jose Peseiro ya maye gurbin Alex Nwobi da Yusuf.
Cote d'Ivoire itama ta saka kwallo a ragar Najeriya
Franck Kessie ya ramawa Cote d'Ivoire cin da Najeriya ta mata. Yanzu ana 1 - 1.
Ya saka kwallon ne yayin da ake buga 'corner kick'
Najeriya ta yi canjinta na farko
Kocin Najeriya Jose Peseiro ya yi canjinsa na farko a wasan karshe na AFCON 2023.
An shigo da Moses Simon yayin da aka fitar da Samuel Chukwueze.
Bidiyo: Shugaba Tinubu ya yi murna yayin da Najeriya ta ci kwallonta na farko
An ga Shugaba Bola Tinubu yana murna a banquet hall yayin da Najeriya ta jefa kwallonta na farko a raga.
An wallafa bidiyon lokacin da shafin NTA na X. Ga bidiyon a kasa:
Najeriya ta jefa kwallo na farko
Kyaftin din Super Eagles William Troost Ekong ya jefa wa Najeriya kwallonta na farko a ragar Elephants na Cote d’Ivoire.
Hotuna daga bikin rufe AFCON
Ga wasu kayatattun hotuna daga bikin rufe gasar ta AFCON.
Dan jarida Pooja ya wallafa wasu hotunan:
Bidiyon abubuwan da suka faru kawo yanzu a AFCON
Ga dan gajeren bodiyon dauke da manyan abubuwan da suka faru a wasannin Super Eagles a AFCON 2023 kawo yanzu.
Ga bidiyon a nan:
Fili ya cika makil yayin da Super Eagles ke shirin tunkarar Elephants na Cote d'Ivoire
Magoya baya sun shirya fafatawar da Super Eagles za ta yi da Elephants na Cote d'Ivoire.
A wani rubutu da ya yi a shafin X, dan jarida Pooja ya ce filin wasan ya cika da magoya baya. Ga bidiyon a nan: