AFCON 2023: Tawagar Najeriya Ta Tsallaka Zuwa Wasan Karshe Bayan Lallasa Afrika Ta Kudu
- Bayan kammala wasa tsakanin Najeriya da Afrika ta Kudu, ta tabbata dai tawagar Super Eagles ce ta tsallaka zuwa wasan karshe
- Wasan ya kare da ci 1-1, amma a zagayen finareti Najeriya ta samu nasara kan Afrika ta Kudu da zura kwallo 4 akan 2
- Mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima ya jinjinawa tawagar Najeriya akan wannan nasara, tare da kara masu kwarin guiwa
Sani Hamza, kwararren edita ne a fanni n nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Tawagar Super Eagles ta Najeriya ta samu nasarar tsallakawa zuwa wasan karshe a gasar cin kofin Nahiyar Afirka, Daily Trust ta ruwaito.
Najeriya ta samu nasarar zuwa wasan karshen ne bayan da ta lallasa tawagar Afrika ta Kudu a wasan kusa da na karshe da aka buga a yau.
Wasan dai ya tashi da ci 1-1 har bayan da aka kammala zagayen ƙarin lokaci inda aka je zagayen buga finareti.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A buga finareti ne golan Najeriya ya samu nasarar kabe kwallaye uku, yayin da Najeriya ta zura kwallo hudu, wanda ya ba ta nasara.
Kokarin da Najeriya ta yi a karawar ta da Afrika ta Kudu ya sa Super Eagles ta kai wasan karshe a kokarinta na ganin ta sake lashe kofin AFCON.
Kashim Shettima ya jinjinawa tawagar Super Eagles
Channels TV ta ruwaito cewa, mataimakin shugaban kasa Kashim Shettima ya yi murna da Super Eagles bayan nasarar da suka samu na doke Bafana Bafana na Afirka ta Kudu.
An kammala wasan ne da ci 1-1 bayan karin lokaci kuma zakaran gasar sau uku za su kara da mai masaukin baki Ivory Coast a wasan karshe a ranar Lahadi.
Bayan nasarar da Najeriya ta samu, mataimakin shugaban kasar ya ziyarci Super Eagles a dakin da ake saka tufafi.
Tinubu ya tura Kashim Shettima zuwa Ivory Coast
Kafin a fara wasan, Legit Hausa ta ruwaito maku yadda shugaba Bola Tinubu ya aika mataimakin shugaban kasar zuwa Ivory Coast domin ya kara kwarin gwiwar ‘yan wasan.
Kasancewar sa a filin wasan ba wai kawai zai kara wa Super Eagles kwarin gwiwa ba ne ba, har ma ya zama wata matattara ga miliyoyin 'yan Najeriya da ke murna daga gidajensu.
Asali: Legit.ng