Kocin Real Madrid Ancelotti ya bayyana wanda ya jawo Barcelona ta yi galaba a El-Clasico

Kocin Real Madrid Ancelotti ya bayyana wanda ya jawo Barcelona ta yi galaba a El-Clasico

  • Carlo Ancelotti ya bayyana cewa kuskuren da ya yi ne ya jawo Barcelona doke Real Madrid a gida
  • Rashin Kareem Benzema ya sa Kocin ya buga 4-4-2, ya yi amfani da Rodrygo da Vinicius Junior
  • Barcelona tayi wa Real Madrid kaca-kaca a filin Santiago Bernabeu bayan ta dade tana neman ci

Spain – Marca ta ce kocin kungiyar Real Madrid, Carlo Ancelotti ya yarda cewa kuskuren da ya yi ne ya jawo masa abin kunya a El Clasico a daren Litinin.

El Clasico shi ne wasan da ake yi tsakanin Real Madrid da manyan abokan gabansu Barcelona a Sifen. Wannan yana cikin wasan da aka fi kallo a Duniya.

A wasan da aka yi a ranar Lahadi, 20 ga watan Maris 2022, kungiyar Barcelona ta samu gagarumar nasara a kan Real Madrid da ci 4-0 a gasan gida.

Kara karanta wannan

Putin ya tsure, ya tattara ma’aikata 1000 ya kora saboda tsoron a sa masa guba a Rasha

Kafin nasarar da ta samu a Madrid a jiya, shekaru uku kenan rabon Barcelona da galaba a El Clasico.

Dabaru sun kwacewa koci

Carlo Ancelotti ya amsa laifinsa, ya ce a sanadiyyarsa ne aka yi wa Real Madrid kaca-kaca.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

Daily Mail ta rahoto Ancelotti mai shekara 62 a Duniya yana fadawa ‘yan jarida bayan an tashi wasan cewa dabaru sun kwace masa, har aka dole kungiyarsa.

“An gagara gane mu a wasan, komai ya jagwalgwale mana. Na fadawa ‘yan wasan cewa rashin nasarar da aka samu laifi na ne.” - Carlo Ancelotti.
Kocin Real Madrid
Carlo Ancelotti Hoto: www.dailymail.co.uk
Asali: UGC

Gwabje Toni Kroos

Rahoton ya ce Ancelotti bai yi magana a game da yadda Pierre-Emerick Aubameyang ya taka ‘dan wasan tsakiyansa watau Toni Kroos, ba tare da an ba shi kati ba.

“Ban fahimci abin da ya faru ba, amma ba zan shiga wannan maganar ba domin ba na bukatar in bada uzuri.”

Kara karanta wannan

Abin Da Ya Sa Aka Yi Min Tiyata, Shugaban NDLEA, Buba Marwa

“Ba mu yi wasa da kyau ba, kuma ba mu tunkari wasan da kyau yadda ya dace ba.” - Ancelotti

Dole mu dage mu ci kofi

“Mu na da isasshen lokacin da za mu kintsa a watanni biyu na karshe domin mu ci kofi. Mun kerewa na biyunmu (Sevilla) da maki tara.
“Na ji haushin wannan rashin nasara, ina ba magoya bayanmu hakuri, amma dole in kwantar da hankalina.” - Carlo Ancelotti

Barcelona ta doke PSG

Abin kunyan da ya faru a Madrid ya biyo bayan Karim Benzema ya ci kwallaye uku a zagayen wasan Real Madrid da kungiyar PSG a gasar Turai a makon jiya.

Kafin ya samu rauni, Benzema ya ci kwallaye 30 a gasar shekarar nan. A kakar 2011/12 ne ya ci mafi yawan kwallayensa a Madrid a karkashin Jose Mourinho.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng