Gasar UCL: Benzema ya ajiye tarihi a Turai, ya bar Mbappe, Messi da PSG da shafa keya
- Karim Benzema ya ci kwallaye uku a zagayen wasan Real Madrid da kungiyar PSG a gasar Turai
- Yanzu Benzema ne ‘dan kwallo mafi tsufa da ya taba cin kwallaye uku a wasa daya a tarihin UCL
- Sabon ‘dan wasan PSG, Lional Messi ya yi shekaru bakwai rabon da ya lashe gasar Turai kenan
Madrid - Karim Benzema ya sake cusa kansa a cikin littafin tarihin kungiyar Real Madrid da ya zura kwallaye uku a cikin mintuna 17 a wasan PSG.
Jaridar Marca ta kasar Sifen ta ce bayan wasan Paris Saint-Germain, Karim Benzema ya sha gaban Alfredo Di Stefano a wajen ci wa Real kwallaye.
A halin yanzu Benzema ya ci kwallaye 30 a gasar shekarar nan. A kakar 2011/12 ne ya ci mafi yawan kwallayensa a Madrid, karkashin Jose Mourinho.
Legit.ng Hausa ta fahimci cewa ‘dan wasan gaban ya taimakawa Real Madrid wajen yin waje da kungiyar PSG daga gasar cin kofin nahiyar Turai a jiya.
Real Madrid ta samu wannan babbar nasara ne bayan Kylian Mbappe ya zura kwallaye biyu a zagaye na farko da na biyu a karawar, kafin wasa ya canza.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Benzema ya karya tarihi
A halin yanzu ‘dan wasan gaban na kasar Faransa yana da kwallaye 309. Shi kuwa gwarzon kungiyar Di Stefano ya zura kwallaye 309 a lokacinsa.
Benzema ya fara leka raga a Madrid a Satumban 2009 lokacin da suka kara da kungiyar Xerez. Ruud van Nistelrooy ne ya taimaka masa ya ci kwallon.
Bayan kusan shekaru 13, Benzema ya sha gaban Raul Gonzalez a wajen adadin kwallaye a Turai. Tsohon kyaftin din ya zura kwallaye 66 da yake wasa.
Yanzu Cristiano Ronaldo ne kurum a gaban ‘dan wasan Faransan a tarihin Real Madrid. Kafin Ronaldo ya tashi, sai da ya ci kwallaye 105 Ronaldo a gasar.
A shekara 34
Opta ta ce a shekara 34 da kwana 80, Benzema ne ‘dan wasa mafi tsufa da ya taba cin kwallaye uku a wasa daya, ya kamo wani tarihin Ferenc Puskas a 1965.
Benzema ya fara buda raga a sakamakon wani kuskure da Gianluigi Donnarumma ya yi a minti na 60. Daga baya ya zura kwallaye biyu a kasa da mintuna biyu.
Barcelona ta bar UCL
Ku na sane da cewa an gama buga dukkanin wasannin zagayen farko na gasar cin kofin nahiyar Turai a Disamba. A halin yanzu an shiga zagaye na gaba a gasar.
Wannan karo Barcelona za ta buga Europa League tare da su AC Milan. Har yanzu dai Man City, Liverpool, Man Utd, Chelsea, Ajax da Bayern su na nan a gasar.
Asali: Legit.ng