'Karin Bayani: Ɗan Ƙasar Habasha Ya Yi Nasara a Gasar Gudun Famfalaƙi Ta Legas a Bana

'Karin Bayani: Ɗan Ƙasar Habasha Ya Yi Nasara a Gasar Gudun Famfalaƙi Ta Legas a Bana

  • Geleta Ulfata dan kasar Habasha ne ya lashe gaar gundun famfalaki na Acces Bank ta Birnin Legas karo na bakwai da aka yi a yau Asabar
  • Ulfata zai tafi gida da kyautan zunzurutun kudi har Dallar Amurka $30,000 bayan nasarar galaban kan sauran mutane 300 da suka yi gasar tare
  • David Barmasai da Emmanuel Naibei duk 'yan kasar Kenya ne suka zo na biyu da na uku inda za su samu $20,000 da $15,000

Legas - Geleta Ulfata na kasar Habasha ya zama zakarar gasar gudun famfalaki karo na bakwai wacce bankin Access ke daukan nauyi mai suna Access Bank Lagos City Marathon, The Cable ta ruwaito.

Ulfafa ya doke sauran masu gudun guda 300 a gasar da aka yi a safiyar ranar Asabar mai tsawon kilomita 42.

Kara karanta wannan

EFCC ta damke Yakubu Musa kan laifin damfarar Surukinsa kudi N3m

Yanzu-Yanzu: Ɗan Ƙasar Habasha Ya Yi Nasara a Gasar Gudun Famfalaƙi Ta Legas a Bana
'Dan Ƙasar Habasha Ya Yi Nasara a Gasar Gudun Famfalaƙi Ta Legas ta 2022. Hoto: @myaccessbank
Asali: Twitter

Zai samu kyautar zunzurutun kudi $30,000.

Yan Kenya ne suka zo na biyu da uku

David Barmasai da Emmanuel Naibei duk 'yan kasar Kenya ne suka zo na biyu da na uku.

Barmasai zai tafi gida da kyautan $20,000 yayin da Naibei zai samu $15,000.

Yar Habasha ce ta yi nasarar a gasar ta mata

Dagne Siranesh Yirga yar kasar Habasha ce mace ta farko da ta fara kammala gudun cikin awa 2 da minti 33 da dakika 50.

Wanda ke biye da ita a mataki na biyu ita ce Alemenseh Guta sanan Naomi Maiyo yar kasar Kenya ta zo na uku.

An fara gudun na kilomita 42 ne daga babban Filin Wasa na Kasa da ke Surulere sannan aka kammala a Eko Atlantic City a Victoria Island.

Kara karanta wannan

Sokoto: Kansila ya gwangwaje 'yan unguwarsa da kyautar tabarmai 2, ya jawo cece-kuce

Naibei da Barmasai ne suka lashe gasar gudun fanfalakin na Access Bank ta Birnin Legas karo na 5 da 6.

Saurari karin bayani ...

Asali: Legit.ng

Authors:
Aminu Ibrahim avatar

Aminu Ibrahim (Hausa HOD) Aminu Ibrahim leads the Hausa Desk at Legit.ng. He holds a Bachelor's degree in Microbiology from Ahmadu Bello University, Zaria, and pursued further with a Master's degree in Environmental Microbiology from Federal University Dutse, Jigawa. With over seven years of experience, Aminu has honed his craft in news reporting and content editing, weaving narratives that captivate and inspire audiences: aminu.ibrahim@corp.legit.ng or +2348030996164

Tags: