Jerin fitattun ciniki 12 da aka yi zuwa ranar karshen cefanen 'Yan wasa a Turai a 2021/22
- A jiya 31 ga watan Junairun 2022 ne aka rufe kasuwar cefanen ‘yan wasan kwallon kafa a Turai
- Mun tattaro fitattun cinikin da aka yi a kakar shekarar nan kamar tashin Aubameyang daga Arsenal
- Kungiyar Tottenham ta rabu da wasu daga cikin ‘yan kwallonta, ta yi sababbin cefane daga Italiya
Jaridar Sporting News ta ce daga cikin mafi shaharan labaran da yake yawo shi ne Christian Eriksen ya samu sabon kulob bayan samun bugun zuciya.
Haka zalika kungiyar Tottenham ta rabu da Tanguy Ndombele da Dele Alli, ta dauko Rodrigo Betancur da Dejan Kulusevski daga kungiyar Juventus.
Kungiyar Arsenal ta samu ta kori babban ‘dan wasan ta Pierre-Emerick Aubameyang, amma ba a ji labarin wanda ta sayo domin ya maye gurbin na sa ba.
Ba a kai ga tabbatar da zuwan Emerick Aubameyang Barcelona ba, amma Fabrizio Romano ya ce an gama komai, Arsenal ta katse kwangilarta da ‘dan wasan.
Dembele ya yi kwantai
Duk da kokarin Barcelona na neman kai da Ousmane Dembele, ba a samu mai son tauraron ba. Shi ma Jese Lingard zai yi zamansa a Manchester United.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Ga wasu daga cikin shahararrun cinikin da aka yi zuwa tsakar daren yau a Turai:
1. P.E. Aubameyang daga Arsenal zuwa Barcelona (kyauta)
2. Christian Eriksen daga Inter Milan zuwa Brentdord (kyauta)
3. Jermain Defoe daga Rangers zuwa Sunderland (kyauta)
4. Dele Alli daga Tottenham zuwa Everton (aro)
5. Julian Alvarez daga River Plate zuwa Man City (kudi $20m)
6. Tanguy Ndombele daga Tottenham zuwa Olympic Lyon (aro)
7. Dejan Kulusevski daga Juventus zuwa Tottenham (aro/kudi £8.3m/£29.2m)
8. Rodrigo Betancur daga Juventus zuwa Tottenham (kudi £21.5m)
9. Fabio Carvalho daga Fulham zuwa Liverpool (kudi kusan €10m)
10. Aaron Ramsey daga Juventus zuwa Rangers (aro_
11. Donny van de Beek daga Manchester United zuwa Everton (aro)
12. Giovani Lo Celso daga Tottenham zuwa Villareal (aro)
AFCON 21
A ranar Lahadi, 23 ga watan Junairu 2022, Najeriya ta gwabza da kasar Tunisiya a gasar cin kofin Afrika, inda aka yi waje da Super Eagles bayan ta sha kashi da ci 0-1.
Rashin ya yi wa 'Yan Najeriya ciwo har an ji tsohon Sanata nan, Shehu Sani yana kuka, ya na cewa ba zai ci abinci ba saboda rashin nasarar da Super Eagles ta samu.
Asali: Legit.ng