Babban ‘Dan wasan Najeriya, Osimhen ya kamu da COVID-19 ana shirin fara gasar AFCON
- An yi gwaji an tabbatar da cewa tauraro Victor Osimhen ya na dauke da kwayar cutar COVID-19
- Kungiyar Napoli ta bada sanarwa cewa Coronavirus ta harbi ‘Dan wasan gaban na Super Eagles
- Idan har Victor Osimhen bai samu lafiya ba, zai yi wahala ya fara bugawa Najeriya a gasar AFCON
Italy - Shirye-shiryen tawagar Super Eagles ya samu tasgaro bayan samun labari an tabbatar da cewa Victor Osimhen ya na dauke da kwayar COVID-19.
Wani rahoto da ya fito daga Goal.com a ranar Alhamis, 30 ga watan Disamba, 2021 ya bayyana cewa gwaji ya nuna Osimhen ya harbu da kwayar cutar.
Kungiyar kwallon kafa na Napoli da ke kasar Italiya ta bada sanarwar wannan labari da ba zai yi wa ‘Yan Najeriya dadi ba a shafinta na yanar gizo a dazu.
“SSC Napoli ta bada sanarwar cewa gwaji ya nuna Victor Osimhen ya na dauke da kwayar Covid-19, amma cutar ba ta fara tasiri a kan shi ba.”
“An shirya cewa Dr. Tartaro zai duba lafiyar ‘dan wasan kwallon kafan a gobe (Juma’a).” - SSC Napoli.
Za a killace 'dan kwallon
Har ila yau, sanarwar tace hukumomi sun umarci Victor Osimhen ya killace kansa, likitoci za su duna shi idan an gano kwayar cutar ta bar jikinsa.
Sai cutar ta rabu da ‘dan wasan gaban na Super Eagles, sannan likitan kungiyar zai duba shi.
Super Eagles ta shiga matsala?
Jaridar Punch tace labarin zai zo a matsayin cikas ga tawagar kwallon kafan Najeriya da ke shiryawa gasar cin kofin nahiyar Afrika da za ayi a Masar.
Victor Osimhen wanda yake tashe a yanzu ne ake sa rai zai jagoranci ‘yan wasan gaban Super Eagles da sun taba lashe gasar kofin nahiyar sau uku a tarihi.
A jerin ‘yan wasan da kocin rikon kwaryan kasar, Augustine Eguavoen ya dauko har da Osimhen. Idan bai warke ba, ba zai buga wasansu da Masar da Sudan ba.
Super Eagles tayi sabon koci
A tsakiyar Disamban nan ne aka ji Hukumar kula da harkar kwallon kafa ta NFF ta bada sanarwar korar babban kocin Super Eagles watau Gernot Rohr.
A jiya aka ji NFF ta nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin 'yan wasan Super Eagles da yarjejeniyar cewa zai karbi aiki bayan an kammala gasar AFCON.
Asali: Legit.ng