Abubuwa 15 da ya dace a sani a kan tsohon kocin Real Madrid da zai jagoranci S/Eagles
- Hukumar kwallon kafan na Najeriya ta nada Jose Peseiro a matsayin sabon kocin Super Eagles
- Peseiro zai karbi aikin horas da ‘yan kwallon kafan Najeriya ne bayan gasar AFCON na shekarar 2022
- Kafin yanzu, Kocin ya yi aiki a Afrika da wasu manyan kungiyoyin kwallon kafa da ake ji da su a Duniya
Nigeria - Goal.com tace Jose Peseiro mai shekara 61 ne zai rike tawagar ‘yan wasan kwallon kafan Najeriya na Super Eagles, bayan an gama gasar AFCON 2022.
Mun tsakuro kadan daga cikin tarihin kocin daga jaridar Daily Trust da shafin na Goal.com.
Buga kwallon kafa
1. An haifi Jose Peseiro a Portugal a 1960, kuma ya buga kwallo a lokacin da yake matashi. Sai dai kocin bai je ko ina ba a lokacin da yake kwallon kafa.
Zamansa koci
2. Ya na shekara 34 a Duniya, Jose Peseiro ya yi ritaya daga kwallo a 1994 ya fara aikin koci. Peseiro bai zama babban koci bas ai a 1999 a CD. Nacional.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
Zuwan Peseiro Madrid
3. A lokacin da Carlos Queiroz ya zama kocin Real Madrid a 2003, Peseiro ya na cikin masu taimaka masa. Sai dai bayan shekara daya duk aka sallame su.
Aikin da ya yi a wasu wurare
4. Daga kasar Sifen sai kocin ya koma gida, inda ya karbi aikin horas da kungiyar Sporting CP.
5. A shekarar 2007 ne Panathinaikos FC ta nada Peseiro a matsayin koci, a nan ma bai dade ba aka kore shi.
6. Bayan shekara guda sai Peseiro ya koma FC Rapid București, daga baya ya ajiye aikin da kansa.
7. Kocin ya yi aiki a matsayin mai horas da ‘yan kwallon kasar Saudi Arabia tsakanin shekarar 2009 da 2011.
8. A watan Yunin 2012 ne Braga ta nada Peseiro a matsayin kocinta. Bayan karshen shekara ta sallame shi.
9. Kocin ya yi aiki da kungiyar Al Wahda FC a UAE daga karshen 2012 zuwa farkon 2015, daga nan ya tafi Masar.
10. Bayan an kore shi daga aiki a Al Ahly, sai kocin ya maye gurbin Julen Lopetegui a kungiyar FC Porto.
11. Har ila yau kocin ya sake komawa Braga duk a shekarar ta 2016, a nan ma bai dade ba aka sake fatattakar shi.
12. A 2017 ne Peseiro ya koma kasar UAE, ya yi aiki da Sharjah FC na watanni tara kafin ya sake rasa aiki.
13. Bayan haka sai kocin ya dawo gida ya karbi aikin horas da Vitória S.C, daga baya ya yi murabus a 2019.
14. A 2020 kasar Venezuela ta nada Peseiro a matsayin kocinta, bayan an gagara biyansa albashi sai ya ajiye aikin.
15. Sabon kocin na Najeriya ya ci kofi hudu a rayuwarsa a kungiyoyin Nacional, Braga, da kuma Al Ahly.
Farautar sabon koci
Dama an ji shugaban hukumar kula da kwallon kafa ta Najeriya, Amaju Pinnick yace su na cigiyar sabon koci bayan an kori Gernot Rohr da 'yan tawagarsa.
Da yake bayani a kan ina aka kwana wajen neman kocin, Amaju Pinnick yace sun yi zama har da kocin AS Roma, Jose Mourinho mai albashin N2bn a duk shekara.
Asali: Legit.ng