Cristiano Ronaldo ya yi abin da babu ‘Dan kwallo mai-ci da ya taba yi, ya zura kwallaye 800
- Cristiano Ronaldo ya ci kwallonsa na 800 a rayuwa, abin da babu wani ‘dan wasa mai-ci da ya taba yi
- ‘Dan wasan gaban na Manchester United ya jefa kwallaye biyu da suka hadu da Arsenal a Old trafford
- Ronaldo ya ci sama da rabin wadannan kwallayen na sa ne lokacin da ya bugawa kungiyar Real Madrid
England - Kwallaye biyu ‘dan wasan gaban kasar Portugal, Cristiano Ronaldo ya zura yayin da Manchester United ta doke kungiyar Arsenal a gasar Firimiya.
Cristiano Ronaldo ya ci kwallayensa na 11 da 12 tun bayan dawowarsa kungiyar Manchester United. Wannan nasara ta ba kungiyar maki uku a teburin BPL.
Legit.ng ta bibiyi wannan wasa inda Ronaldo ya ci kwallon farko a minti na 52. A kusan minti na 70, Ronaldo ya samu damar buga finariti, ya saida Aaron Ramsdale.
Wannan ya na nufin Ronaldo ya ci kwallayensa na 800 da 801 tun da ya fara buga kwallon kafa.
Abin da tsofaffin 'yan wasa su ke fada
Da yake maida martani a Twitter, tsohon abokin wasan Ronaldo watau Rio Ferdinand, ya caccaki masu sukar fitaccen ‘dan wasan gaban mai shekara 36 a Duniya.
Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!
“Eh lallai, Cristiano ne matsalar. Na ga alama. #MUNARS — Rio Ferdinand (@rioferdy5), 2 ga watan Disamba, 2021.
Shi ma Thierry Henry da yake magana a Amazon Prime, ya yabi ‘dan wasan da ya ci tsohon kulob dinsa. Har Henry ya yi ritaya, kwallaye 417 ya ci a rayuwarsa.
“Sai dai kurum ka zauna ka ce ‘Ikon Allah’, ka yabawa wannan mutum.” – Alan Shearer.
Babu wanda ya fi Ronaldo kwallaye?
Kamar yadda BBC ta fitar da rahoto, Ronaldo ne wanda ya fi kowa yawan kwallaye yanzu a Duniya, haka zalika shi ne gaba a gasar Turai da tarihin Real Madrid.
Rahoton yace ana ikirarin Josef Bican ya ci kwallaye 821 a rayuwarsa. Amma zance mafi inganci shi ne kwallaye 805 ya zura a raga idan aka cire kananan wasanni.
Ana kuma cewa Pele da Romario sun ci kwallo sama da 1, 000. Su ma dai ana rage adadin zuwa 700 idan ana maganar manyan wasannin da suka buga a lokacinsu.
Ronaldo zai je Qatar 2022
Mako daya kenan da ku ka ji labari cewa Hukumar kwallon kafa ta hada Portugal da kasar Italiya a rukuni daya na zuwa gasar kofin Duniya wanda za ayi a kasar Qatar.
FIFA ta shirya duron gasar cin kofi na kasashen Duniya, inda aka hada Italiya da Portugal a rukuni guda, hakan ya na nufin daya kadai ne zai yi nasarar buga kofin.
Asali: Legit.ng