Yan Fashi Da Makami
Rundunar 'yan sanda ta tabbatar da cewa 'yan bindiga sun yi garkuwa da daliban kwalejin kiwon lafiya ta jihar Enugu a wani hari da suka kai yammacin ranar Alhamis.
Ma'aikatar shari'a ta Kano ta tafka asara bayan masu zanga-zanga sun kutsa cikinta tare da sace muhimman abubuwa daga cikin akwai kudi masu yawa da bindigu.
Kwamishinan ƴan sandan birnin tarayya Abuja ya tabbatar da cafke mutum biyu da ake zargin da fashi da makami bayan kashe abokansu biyu a Mabushi.
Gwamnatin Kano ta maka wasu jami'an 'yan sanda guda uku a gaban kotu bisa zargin aikata fashi da makami a jihar, inda su ka yi fashin N322m, an mayar da wasu
Rundunar ‘yan sandan kasar nan ta bayyana samun nasara kan wasu miyagu da ke taimakawa ‘yan ta’adda su na muzgunawa al’umaar kasar nan a babban birnin tarayya Abuja.
Rundunar yan sandan Kano ta cafke wasu mutane 19 da ake zargi da aikata mugayen laifuka iri daban-daban a jihar, ciki har da fashi da makami da satar mutane.
Babbar kotun jihar Ekiti ta yanke hukuncin kisa ta hanyar rataya ga wasu 'yan fashi da makami guda uku. Kotun ta ce an yanke musu hukunci ne bayan kama su da laifi.
Rundunar ‘yan sandan jihar Kano ta gargadi matasa da su guji tada zaune tsaye a cikin watan Ramadan, musamman a lokacin gudanar da wasannin al’ada na “tashe”.
Hukumar Kwastam a tsibirin Tin-Can da ke jihar Legas ta yi nasarar dakile kokarin shigo da muggan makamai da miyagun kwayoyi Najeriya a yau Juma'a.
Yan Fashi Da Makami
Samu kari