Siyasar Najeriya
INEC ta sa wa’adin fidda gwani daga 20 ga Maris zuwa 10 ga Afrilu, ta bukaci jam’iyyu su bi ka’ida don gujewa matsaloli da ka iya hana gudanar da sahihin zabe.
Rigima tsakanin Majalisar dokokin jihar Ribas da ɓangaren gwamnati ta kara tsanani, ƴan tsagin Wike na shirin dawo da yunƙurinsu na tsige Gwamna Fubara.
Majalisar dattawa ta amince da shawarwarin kwamitin ladabtarwarta, inda ta dakatar da sanatar Kogi ta Tsakiya, Sanata Natasha, wadda ta zargi Akpabio da lalata.
Tsohon mataimakin shugaban jam'iyyar PDP na kasa, Bode George, ya bayyana cewa abu ne mai sauki a kayar da Bola Tinubu da APC a zaben shekarar 2027.
Wasu da ake zargin masu goyon bayan Sanata Babangida Hussaini a Jigawa sun yi wa tsohon hadimin Badaru Abubakar duka kan sukar mai gidansu a gidan rediyo.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi bayani ta bangarensa kan zargin da ake masa na neman Sanata Natasha da lalata, ya ce karya ne.
Mataimakiyar gwamnan jihar Ribas, Farfesa Ngozi Odu ta musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa ta yi murabus daga matsayinsa saboda matsin lambar da take sha.
PDP ta kori Sanata Adolphus Wabara bisa zargin cin amanar jam’iyya, amma kotu ta dakatar da hukuncin. Yanzu haka dai ana jiran matakin PDP ta kasa kan lamarin.
Gwamna Adeleke ya gana da Bisi Akande kan rikicin kananan hukumomi, yana mai cewa gwamnatinsa na bin doka. Akande ya bukaci zaman lafiya da bin doka a Osun.
Siyasar Najeriya
Samu kari