Siyasar Najeriya
Yayin da ministar mata ke ganin hakan ba daidai bane, kakakin majalisar dokokin jihar Niger, Abdulmalik Sarkin Daji ya fasa ɗaukar nauyin auren mata marayu 100.
Bello El-Rufai, ɗan tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmed El-Rufai, ya ce ko kaɗan babu hannunsa a kwangilolin da mahaifinsa ya bayar a mulkinsa.
Kwanaki bayan jam'iyyar YPP ta dakatar da su, wasu 'yan majalisar jihar Abia guda 2, Hon. Iheanacho Nwogu da Hon. Fyne Ahuama sun sauya sheka zuwa Labour.
Kotun sauraron ƙararrakin zaɓen gwamnan jihar Kogi da ke zamanta a Abuja ta kammala sauraron karar da Ajaka ya kalubalanci nasarar Gwamna Ahmed Ododo.
Tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Alhaji Atiku Abubakar, ya ce ya yi farin cikin karɓar bakuncin tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi na jam'iyyar Labour Party.
Yayin da ake tunkarar zaben gwamna a jihar Edo a 2024, jam'iyyar PDO ta rasa ɗaya daga cikin manyan jiga-jiganta, Mista Idahosa ya koma jam'iyar APC.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa a zaben 2023, Peter Obi ya kai ziyara ga tsohon gwamnan jihar Jigawa yayin da aka fara jita-jitar zai sauya sheƙa zuwa PDP.
Yayin da rigima ke kara tsananta a jihar Rivers, Sir Siminaliya Fubara ya sha alwashin kafa kwamitin da zai binciki tsohuwar gwamnatin jihar mai arzikin Fetur.
Sakataren gwamnatin tarayya, Sanata George Akume, ya tarbi tsohon minista, Farfesa Hagher wanda ya sauya sheƙa daga PDP zuwa APC a birnin tarayya Abuja.
Siyasar Najeriya
Samu kari