
Haduran mota a Najeriya







Hukumar kiyaye hadurra ta kasa (FRSC) reshen jihar Ondo , ta tabbatar da aukuwar wani mummunan hatsarin mota wanda ya salwantar da rayukan mutum16.

Mutum ɗaya ya rasa ransa a karshen makonnan a jihar Bayelsa lokacin da wani jirgin ruwa ya kife bayan ya ɗauko mutane a yankin karamar hukumar Ijaw ta Kudu.

An samu hadarin babbar mota tirela a jihar Ogun inda tsohuwa da jikarta suka rasu bayan tirela ta markade su har lahira. Wadanda suka ji rauni suna kwance a asibiti.

Masu ababen hawa da ke bin titin Anthony Oke zuwa Gbagada ta babbar hanyar Oshodi-Apapa sun tsallake rijiya da baya yayin da yanka dauke da gas ta fadi.

An tafka gagarumar asarar rayuka a jihar Kaduna bayan motoci biyu sun yi taho mu gama da juna a Zaria inda mutane 11 su ka rasu nan take, mutum hudu kuma na asibiti.

Rundunar yan samda a jihar Jigawa ta tabbatar da faruwar hadarin mota da ya faru a hanyar kasuwar Kanya kuma ya jawo asarar rayuka 14 da jikkata mutane da dama.

Shugaban jami'ar kimiyya da fasaha ta Enugu, Farfesa Aloysius Michaels ya gano abin da ya fi kashe 'yan Najeriya tsakanin 'yan ta'adda da rashin kyawun hanyoyi.

An samu mummunan hadarin mota a jihar Kano a safiyar yau Litinin inda mutane kimanin 30 suka mutu, 53 suna kwance a asibitin Murtala. FRSC ta tabbatar da lamarin.

Mutanen da ke kusa da Dangwaro flyover a kusa da titin Kano-Zaria sun shiga tashin hankali bayan hadarin babbar mota ya kashe mutane akalla 25 har lahira.
Haduran mota a Najeriya
Samu kari