Jihar Ondo
Gwamnan jihar Ondo, Lucky Aiyedatiwa ya sallami dukkan kwamishinoni da sauran hadimai da masu rike da mukaman siyasa a jihar don inganta harkokin gwamnati.
Wani mutumi ya ce ga garin ku nan bayan ya gama sheke ayarsa da wata mata a otal. Rundunar yan sandan jihar ta cafke mutum biyu da ake zargi da hannunsu a lamarin.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa ya gana da masu faɗa a ji na jam'iyyar APC mai mulki yayin da ake tunkarar babban zaben gwamnan jihar a wannan shekara ta 2024.
Masu garkuwa da mutane sun sace wasu mutane da ba a san adadinsu ba a hanyar titin Akure/Ikere. Jami'ar Yan sanda Funmi Odunlami ta tabbatar da lamarin.
Jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya ta bayyana cewa ba za ta bai wa Gwamna Lucky Aiyedatiwa tikiti haka kawai ba hammaya ba sai dai shima ya nema kamar kowa.
Rikicin siyasa a jihar Ondo na kara tabarbarewa tun bayan gudanar da zaben fidda gwani a jihar don cike gurbin mazabar Akoko a Majalisar Tarayya.
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya shirya yin garambawul a mukaman gwamnatinsa bayan rasuwar tsohon gwamnan jihar, Rotimi Akeredolu a watan Disamba.
Allen Sawore, tsohon mai taimakawa gwamnan jihar Ondo kan harkonin midiya ya sanar da ficewa daga babbar jam'iyyar adawa PDP saboda rigingimun cikin gida.
An sake samun hatsaniya bayan an zabi dan tsohon Sifetan 'yan sanda a matsayin wanda zai gaji kujerar Ministan Tinubu bayan ya yi murabus daga kujerar.
Jihar Ondo
Samu kari