Ogun
Bayan zargin cin zarafin jami'an gwamnati, rundunar ‘yan sanda a Ogun ta ayyana fitaccen mawaki Habeeb Okikiola a matsayin wanda ake nema ruwa a jallo.
An tsinci gawar Sufera Haruna Mohammed a wani dakin otal a Ogun. An fara bincike don gano macen da suka shigo tare da shi da sanin musabbabin mutuwarsa.
Rundunar Amotekun ta ceto ‘yan mata daga wani gidan karuwa a Ogun. 'Yan matan sun ce suna lalata da maza 10 zuwa 12 a rana kuma ana biyansu N1000 zuwa N5000.
Sarkin masarautar Olugbo a jihar Ogun, Mai Martaba Frederick Obateru Eniolorunda Akinruntanya musanta labarin da ake yaɗawa cewa Allah ya masa rasuwa.
Atiku Abubakar ya gana da tsohon Shugaban Kasa Obasanjo a Abeokuta. Ana hasashen tattaunawar ta shafi shirye-shiryen tunkarar zaben 2027 tare da sauran ‘yan hamayya.
Gwamnan jihar Ogun ya yi jimamin rasuwar sarkin, Iperu-Remo, Oba Adeleke Adelekan Idowu-Basibo, ya ce wannan rashi ne da zai wahala a iya maye gurbinsa.
Mai martaba sarki na masarautar Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi ya tsinci kansa a gidan gyaran hali bayan gaza cika sharuddan belin da aka ba shi a Ogun.
Rundunar ƴan sandan jihar Ogun ta gurfanar da wani dattijo a gabam kuliya kan tuhumar haɗin kai, cin zarafin wani bawan Allah, kotu ta ɗage zaman.
Bayan zargin cin zarafi da wani basarake ya yi, Gwamnatin jihar Ogun ta dakatar da Oba Abdulsemiu Ogunjobi na Orile Ifo na tsawon watanni shida daga sarauta.
Ogun
Samu kari