Sarkin Kano
Yayin da ake cikin ruɗani umarnin kotuna da suka sha banban, ɗan takarar gwamna inuwar jam'iyyar NNPP a jihar Ogun, Ajadi ya yaba da dawowar Sanusi II.
Wata kotun tarayya da ke zamanta a Kano ta ba da umarnin a fitar sa Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II, daga fadar Sarkin Kano ta Gidan Rumfa.
Wata babbar kotun jihar Kano ta hana jami'an tsaro na 'yan sanda, DSS da sojoji fitar da Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II daga fadar Sarki ko cafke shi.
Kungiyar kwararrun ma'aikata a Arewacin Najeriya (NPF) ta roki Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero ya rungumi kaddara sauke shi da gwamnati ta yi.
Wasu lauyoyi, wadanda suka bayyana kan su a matsayin 'kungiyar lauyoyin Arewa' sun ba gwamnan Kano Abba Yusuf wa'adin awa 48 ya tsige Sarki Muhammadu Sanusi II.
Danbalki Kwamanda ya bukaci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya sa baki a rikicin sarautar da ke faruwa a jihar Kano tun kafin gwamna ya lalata komai.
Gwamnatin Kano ta dakatar da shugaban gidan talabijin na Abubakar Rimi (ARTV), Mustapha Indabawa sabod zargin rashawa. ta maye gurbinsa da Hajiya Hauwa Ibrahim.
Yayin da gwamnatin Kano ta nemi alfarma wurin Bola Tinubu, shugaban ya yi biris, zai yi jawabi a taron majalisun Tarayya biyu kan nasarar dimukradiyya.
Ba da umarnin dakatar da mayar da Muhammadu Sanusi II a matsayin Sarkin Kano ba shi ne karon farko da Mai shari'a A.M Liman ya shiga cikin cakwakiya ba.
Sarkin Kano
Samu kari