Matasan Najeriya
Hajiya Lami Adamu Lau, shugabar kungiyar mata ta ƙasa ta kwanta dama a lokacin da ta je jihar Kebbi domin gudanar da wasu ayyuka, gwamnan Taraba ya yi alhini.
Rundunar tsaron fafar hula reshen jihar Kano ta kama wasu mutane biyu da ake zargi da barnatar wayoyin fitilun kan titi a yankin karamar hukumar Fagge.
A ci gaba da tsaftace kafafen sada zumunta da hukumar Hisbah ta jihar Kano ta soma, ta sake cafke dan TikTok din nan Rabi'u Sulaiman, da aka fi sani da Lawancy.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke mawakin nan kuma Jarumin TikTok Al’amin G-Fresh saboda zargin yi wa Alkur’ani Mai Girma Izgili da kuma yin kalaman batsa.
Yayin da ake cikin mummunan yanayi a Najeriya, tsohon shugaban kasa, Cif Olusegun Obasano ya nemo mafita ga rashin shugabanci da ake fama da shi a kasar.
Bayan Shugaba Bola Tinubu ya tabbatar da sauya taken Najeriya, hukumar wayar da kan jama'a ta NOA ta bukaci jami'anta su haddace sabon taken cikin kwanaki uku.
Wasu matasa a yankin masarautar Okuku a jihar Kuros Riba sun nuna damuwa da halin sarkin yankinsu saboda ya ƙi ya shawo kan rikicin ƙabilancin da ke faruwa.
Firaministan Birtaniya, Rishi Sunak ya yi magana kan cewa a yau ba sai mutum ya mallaki digiri zai yi nasara ba. Mutane na mayar masa da martani daga fadin duniya.
Tsohuwar ministar ilimi a Najeriya Obiageli Ezekwesili ta ce babu abin da zai sa ta koma rera tsohon taken Najeriya da aka dawo da shi ya maye gurbin na yanzu.
Matasan Najeriya
Samu kari