Hukumar gidajen yarin Najeriya
Kotu ta ba da belin tsohon ɗan sanda, DCP Abba Kyari bayan shafe watanni 27 a gidan gyaran hali kan zargin alaka da manyan masu hada-hadar miyagun kwayoyi.
Kwamishinan 'yan sandan Kano ya bayyana cewa daurarru kimanin 400 dake gidan yarin kurmawa a Kano ba su san makomarsu ba. Da yawansu takardar tuhumarsu ta bata.
Rahotanni sun nuna cewa fursunoni da dama sun tsere daga gidan gyaran hali na Suleja da ke jihar Neja bayan da ruwan sama ya lalata katangar ginin gidan yarin.
Fitaccen ɗan daudu a Najeriya, Idris Okuneye da aka fi sani da Bobrisky ya nemi alfarma bayan daure shi har tsawon watanni shida a gidan kaso kan cin mutuncin naira.
Wani babban ganduroba da ya yi magana da ‘yan jarida kan halin Bobrisky a gidan yari ya ce yana kiyaye duk ka’idojin gidan yarin kuma namiji ne ba mata maza ba.
Hukumar kula da gidajen yari a Najeriya, NCS ta ce za ta bi shaidar da ta samu daga kotu kan fitaccen ɗan daudu, Idris Bobrisky wurin ajiye shi a bangaren maza.
A ranar Laraba, 27 ga watan Maris, kotu ta garkame shugaban kungiyar kwadago ta NLC reshen jihar Yobe, Kwamared Muktar Tarbutu bisa zargin karkatar da kayan tallafi.
Wani fursuna a gidan yarin Oke-Kura a Ilorin babban birnin jihar Kwara ya harbe wani bakanike da ke tsaye a gefen hanya. Lamarin dai ya faru ne a ranar Juma'a.
Kotu ta yi hukunci kan shari’ar Hafsat 'Chuchu' da Nafiu Hafizuinda ta umarci sake duba lafiyar kwakwalwar Hafsat da ake zargi da kisan kai a Kano.
Hukumar gidajen yarin Najeriya
Samu kari