Hukumar gidajen yarin Najeriya
A labarin nan, za a ji cewa hukumar ajiya da gyaran gidan hali ta jihar Kano ta yi magana a kan barin fursunoni su ci gaba da kada kuri'a a lokutan zabe a Najeriya.
Bayan tserewar fursunoni 16 daga gidajen yari a Keffi, an tuno yadda aka fasa gidajen yari 10 daga 2020 zuwa 2025 da adadin fursunonin da suka tsere a hare-haren.
Fursunoni 16 sun tsere daga gidan gyaran hali na Keffi, an ce an sake kama bakwai daga cikin su, yayin da shugaban NCoS ya sha alwashin hukunta masu hannu a lamarin.
Mutane miliyan 1.91 sun nemi guraben aiki 30,000 na CDCFIB, inda Kogi ta fi yawan masu nema, sannan hukumar ta ce za a yi amfani da cancanta wajen daukar aiki.
Gwamnatin tarayya ta yanke hukuncin korar ma'aikatan hukumar gyaran hali ta ƙasa su 15, ta kuma rage wa wasu 59 matsayi saboda aikata laifuka da rashin ɗa'a.
Majiyoyi sun tabbatar da cewa babbar kotun tarayya da ke jihar Kano ta yi zama kan shari'ar da ake yi game da dan TikTok, Abubakar Ibrahim da aka fi sani da G-Fresh.
Rahotanni sun bayyana cewa an tura malamar addinin Musulunci daga Ibadan, Alhaja Kafilat Kaola gidan gyaran hali na Oke Kura a Ilorin a jihar Kwara.
Gwamnatin Najeriya ta dage ɗaukar ma'aikata a Immigration, Civil Defence, da sauransu zuwa 14 ga Yuli, 2025. A cewar sanarwar, an samar da sabon shafin neman aikin.
Bayan zargin batanci da ake yi masa, wata kotu a Ede da ke jihar Osun, ta bayar da umarnin tsare wani babban basarake da aka dakatar, Jimoh Abdulkabir.
Hukumar gidajen yarin Najeriya
Samu kari