Hukumar gidajen yarin Najeriya
Wasu fursunoni sun lallaɓa, sun bi dare tare da tsere wa daga gidan yarin tarayya da ke jihar Kogi, kuma tuni jami'an tsaro sun shiga kokarin cafko su.
Shugaba Tinubu ya amince da daukar likitoci 50 da malaman jinya 100 don kula da lafiyar fursunoni, tare da gyaran gidan yarin Kuje da sabbin wuraren kiwon lafiya.
Jami'i a kamfanin Binance, Tigran Gambaryan, ya bayyana yadda tsohon mataimakin kwamishinan yan sanda, Abba Kyari ya taimaka masa a gidan yari na Kuje.
Mai martaba sarki na masarautar Orile Ifo, Oba Abdulsemiu Ogunjobi ya tsinci kansa a gidan gyaran hali bayan gaza cika sharuddan belin da aka ba shi a Ogun.
Nasir El-Rufai ya ziyarci Bashir Saidu a gidan gyaran hali na Kaduna, amma tsohon gwamnan ya ki cewa komai game da zargin da ake yiwa Bashir na almundahana.
Gwamnatin jihar Ondo ta sha alwashin daukar mummunan mataki kan wasu sarakunan gargajiya kan laifin kwace filaye inda ta ce za ta tura su gidan kaso.
Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya amince da naɗin Nwakuche Ndidi a matssyin muƙaddashin konturola janar na hukumar kula da gidajen gyaran hali.
Tsohon sanata daga jihar Ekiti mai suna Babafemi Ojudu ya ce har fitsari ya sha a gidan yari domin ya rayu bayan cafke shi da aka yi a mulkin Sani Abacha.
Tsohon shugaban kasa, Janar Yakubu Gowon ya bayyana jin dadinsa da ganin Olusegun Obasanjo ya mulki Najeriya a 1999 bayan ya fito daga gidan yari.
Hukumar gidajen yarin Najeriya
Samu kari