Malaman Izala da darika
Kungiyar Izala reshen Kankia ya sanar da rufe masallacin Juma'a sakamakon ambaliyar ruwan da ta mamaye shi, ta fara shirye shiryen gina sabon masallaci.
Gwamnatin jihar Neja ta bayyana cewa jita-jitar da ake yadawa cewaGwamna Umaru Bago ya hana malamai wa'azi sai sun mallaki lasisi ba gaskiya ba ne.
Gwamnatin jihar Neja ta kafa dokar hana wa'azi ba tare da lasisi ba. Ana bukatar kowane malami ya nemi izini daga hukumar kula da addini kafin cikar wata biyu.
A labarin nan, za a ji cewa gwamna Abba Kabir Yusuf zai kaddamar da Majalisar Shura da ake sa ran zai taimaka wa gwamnatin wajen gano matsalolin jama'a.
Yayin da ake maganar hada kan malaman Izalah da darika, Sheikh Ishaq Adam Ishaq ya bayyana matsayarsa kan lamarin a faifan bidiyo inda ya soki shirin.
Gwamnatin Sokoto ta kaddamar da biyan alawus ga limamai da ladanai tare da tallafa wa masallatan Juma’a domin karfafa addini da koyar da Alkur’ani.
Gwamnan jihar Katsina, Dikko Umaru Radda zai rika biyan limaman masallatai da masu sharar masallaci alawus a Katsina. Za a kara wa dagatai albashi da masu unguwa.
Rundunar ’yan sanda Jigawa ta dauki tsauraran matakan tsaro don bikin Mauludi, inda CP Dahiru ya bukaci jama’a su gudanar da bukukuwa cikin lumana.
Shugaban kwamitin amintattu na kungiyar Izala, Sheikh Yakubu Musa Hassan Katsina Sautus Sunna ya fadi alakarsa da jagoran Darikar Tijjaniyya, Ibrahim Inyass.
Malaman Izala da darika
Samu kari