Hukumar Sojin Najeriya
Hedkwatar tsaron Najeriya ta bayyana cewa yayin samamen haɗin guiwa na sojoji an yi nasarar kashe ƴan bindigan da suka sace ɗaliban makarantar Kuriga.
Mai Martaba Clement Oghenerukevwe Ikolo, Urhukpe 1, ya mika kansa ga ‘yan sandan jihar Delta, bayan da aka alakanta shi da sa hannu a kashe sojojin Najeriya.
Hedikwatar tsaro ta ce ta mika mutane 313 da ta kama ga gwamnatin Borno bisa umarnin babbar kotun tarayya da ke zamanta a Maiduguri. An gane mutanen ba su da laifi.
A jiya Laraba 27 ga watan Maris aka yi ta yada jita-jitar cewa hatsabibin ɗan bindiga, Dogo Giɗe ya mutu a jihar Sokoto, an samu karin bayani kan labarin.
Dakarun sojoji a Najeriya sun wallafa sunayen mutane takwas da suke nema ruwa a jallo kan kisan sojoji a jihar Delta ciki har da wani Farfesa da wata mata.
Rundunar sojojin Nigeriya ta sanar da murƙushe hatsabibin ɗan bindiga a jihar Zamfara, Junaidu Fasagora tare da mayaƙansa da dama a karamar hukumar Tsare.
Hadimini shugaban kasa, Bola Tinubu a bangaren sadarwa, Bayo Onanuga ya soki Muhammadu Buhari kan rashin mutunta sojojin da suka mutu a bakin aiki.
Shugaban kasa, Bola Tinubu ya umarci dattawa da kuma sarakunan kauyen Okuama da ke jihar Delta da su zakulo wadanda suka aikata wannan ta'asar a jihar.
Shugaban kasa Bola Tinubu zai halarci jana’izar sojojin Najeriya da aka kashe a yankin Okuama da ke karamar hukumar Ughelli ta Kudu a jihar Delta.
Hukumar Sojin Najeriya
Samu kari