NLC
Gwamnatin Bola Tinubu ta fara biyan ma'aikata mafi karancin albashi na N70,000 a watan Satumba. Bola Tinubu ya fara biyan sabon albashi ne ga ma'aikatan tarayya.
Kungiyar kwadago ta kasa (NLC) reshen jihar Akwa Ibom ta fara yajin aiki a fadin jihar. NLC ta fara yajin ne sakamakon tashin gwauron zabin da farashin fetur ya yi.
Kungiyar kwadago ta ce Bola Tinubu ya so biya musu kudin jirgi domin zuwa kasahe su ji kudin man fetur amma suka ki kar ace sun karbi cin hanci da rashawa.
Kungiyar kwadago ta ce N70,000 da za a biya ma'aikata ba za ta tsinana komai ba kasancewar an kara kudin fetur. Shugaban yan kwadago ya ce za su zauna da Tinubu
Kungiyar yan fansho ta yi watsi da mafi karancin albashi na N70,000 da gwamnatin tarayya ta yi. Sun bukaci yan kwadago su tilasta gwamnati biyan N250,000.
Gwamnatin Ebonyi ta yi alkawarin fara biyan ma'aikata sabon mafi karancin albashi na N70,000 a watan Satumba. Gwamnatin ta ce tana jira a kammala hada rahoto.
Gwamnatin jihar Kogi karƙashin jagorancin Ahmed Usman Ododo ta kafa kwamitim zai jagoranci yadda za a fata biyan ma'aikata sabon albashi mafi ƙaranci.
Ana zargin DSS da cin zarafin al'ummar Najeriya ba bisa ka'ida ba wanda ya zama ruwan dare kama daga mamayar ofishin SERAP zuwa cafke shugaban NLC, Joe Ajaero.
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa aiki ya yi nisa kan batun tsara taswirar da za a bi wajen biyan sabon mafi ƙarancin albashi na N70,000 a Najeriya.
NLC
Samu kari