Hukumar yan sandan NAjeriya
Kakakin ‘yan sandan jihar Taraba, Abdullahi Usman, ya rasu da safiyar Lahadi. An shirya jana’izarsa da karfe 2 na rana a makabartar ‘yan sanda Jalingo.
Basarake a Ilawe-Ekiti, Ajibade Olubunmi, ya ce an yi masa barazanar kisa yayin wata ganawar danginsu a ranar 15 ga Maris inda ya yi korafi ga yan sanda.
‘Yan sanda sun kama mutum 12 kan harin masallaci a Rigasa. An ce 'yan daba sun bi wani matashi har cikin masallacin, suka daba masa wuka har lahira ana Sallah.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kai harin ta'addanci kan 'yan sa-kai a jihar Zamfara. 'Yan bindigan sun hallaka jami'an tsaro masu yawa a yayin harin.
Wasu miyagun 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a babban birnin tarayya Abuja. 'Yan bindigan sun yi awon gaba da wata soja da wasu mutum biyu.
Bayan rigima ta barke a Osun, gwamnatin jihar ta sake kakabawa garuruwan Ifon da Ilobu dokar hana fita daga karfe 6 na yamma zuwa 6 na safe saboda dalilan tsaro.
Sufeton 'yan sandan Najeriya ya yi gargadin cewa za su yi maganin masu son tayar da zaune tsaye a Rivers bayan dakatar da gwamna Siminalayi Fubara.
‘Yan bindiga sun sace dalibai 2 a jami’ar FUDMA, da ke jihar Katsina yayin da aka ceto wani wanda aka yi garkuwa da shi a Adamawa, an kuma kama malami a Jigawa.
‘Yan sanda sun kama masu safarar makamai, miyagun kwayoyi da jabun kuɗi a samame daban-daban, inda suka cafke masu hannu a laifuka tare da kayayyakin haram.
Hukumar yan sandan NAjeriya
Samu kari