Musulmai
Shugaba Tinubu ya tura sakon jaje ga iyalan marigayi Baba Adinni na Legas, Sheikh Abdul-Afis Aṣamu bayan ya rasu da daren jiya Talata a jihar Legas.
Babban malamin Musulunci a jihar Oyo, Sheikh Abdulfatai Muhali Alaga ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 80 a duniya a yau Talata a Ibadan.
Tsohon Atoni-janar na farko a jihar Kwara kuma kwamishinan Shari'a, Alhaji Alarape Salman ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 81 a duniya a jiya Lahadi.
Wata budurwa, Zeinab Khenyab a kasar Iran ta fuskanci daurin shekaru biyu a gidan kaso bayan ana zagin ta wallafa hotonta ba tare da sanya dankwali ba.
Kungiyar MURIC ta bukaci yan majalisa da su fara rabon buhuhunan shinkafa da sauran kayan abinci da shuka karba daga wajen Shugaban kasa Bola Tinubu.
Limamin masallaci a New Jersey da aka harba da bindiga ya rigamu gidan gaskiya a ranar Laraba, kamar yadda hukumar jihar ta sanar. Har yanzu ana kan yin bincike.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata babbar mota makare da kwalaben barasa fiye da dubu 24 da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri da tsakar dare.
A karshe, Gwamna Dauda Lawal ya shiga tsakani bayan rikicin masallacin da ya jawo shafe shekaru bakwai a rufe kan rikicin akida a garin Moriki a jihar Zamfara.
Alhaji Sa'ad Abubakar III ya ce jami'an tsaro da gwamnati ba sa iya samun bayanan sirri har sai 'yan bindiga sun gama cin karensu ba babbaka, ya nemi a gyara.
Musulmai
Samu kari