Malaman Makaranta
Wata 'yar Najeriya dake aikin koyarwa a kasar Japan ta nuna takaicinta kan yadda dalibanta ke kiranta da biri saboda nuna banbancin launin fata. Tace ta gaji.
Gwamnatin jihar Taraba ta hannun ma'aikatar ilimin jihar ta dakatar da shugabannin makarantun sakandare 7 bayan kama su suna karbar kudi daga hannun dalibai.
Hukumar shirya jarrabawar shiga manyan makarantu (JAMB) ta bayyana cewa ta gano dubannan matasan kasar nan da ke karyar sun kammala manyan makarantu.
'Yan bindiga sun kai hari gidan wani malamin jami’ar tarayya ta Dutsinma (FUDMA) da ke Katsina. An ce 'yan ta'addan sun kashe malamin, sun kuma tafi da yaransa biyu.
Ministan Ilimi a Najeriya, Farfesa Tahir Mamman ya bukaci kungiyoyi masu zaman kansu su yi koyi da Dakta Emeka Offor wajen tallafawa harkar ilimi a Najeriya.
Kungiyar malaman jami’a da aka fi sani da ASUU, ta jawo hankalin jama’a game da abin da ke faruwa a jami’ar SAZU, ana barin makarantar saboda rashin tsarin fansho.
Gwamnatin jihar Kano za ta kashe kudi kimanin N4.8b wajen gyaran makarantu da sababbin gine-gine. Za kuma ta dauki ma'aikata kusan 2000 a makarantun jihar.
Kungiyoyin ma’aikatan jami’o’in Najeriya sun ba gwamnatin tarayya wa’adin mako biyu da ta biya su albashin watanni hudu da ta rike ko ta fuskanci fushin kungiyoyin.
Gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana yadda ta ke kashe N4b domin ciyar da dalibai 25,000 a makarantun kwana a jihar. Dakta Fauziyya Ada ce ta bayyana haka.
Malaman Makaranta
Samu kari