Labarin Sojojin Najeriya
Rundunar sojin Najeriya ta tabbatar da kame sojan da ya caccaki Gwamna Babajide Sanwo-Olu na jihar Legas bayan ya dauki wani mataki kan sojan da ya saba doka.
A cewar tsohon mataimakin sufeta janar na 'yan sanda, Dabup Makama, sun sanar da jami'an tsaro cewa 'yan ta'adda za su kai hari Filato amma suka yi biris da rahoton.
Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani, ya yi magana da kaushin murya kan hare-haren da yan bindiga suka kai a wasu kauyukan jihar inda suka halaka mutane.
Dakarun sojojin Najeriya sun samu nasarar halaka yan ta'adda 10 a wata fafatawa da suka yi a jihar Katsina. Sojojin sun kuma ceto mutanen da aka sace aZamfara.
Hedikwatar tsaro ta ƙasa DHQ ta bayyana dumbin nasarorin da rundunar sojin Najeriya ta samu a hare-haren kwantan ɓauna da samame kan yan ta'adda a mako ɗaya.
Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya nusar da mata kan muhimmancin shiga aikin soja musamman nan a sojan kasa. Ya ce an bar su a baya a wurare da dama.
Wasu matasa shida daga jihar Kaduna za su fuskanci fushin gwamnatin jihar Legas kan takardun bogi. Matasan sun yi amfani da takardun zama 'yan Legas ne.
Rundunar tsaro Operation Safe Haven (OPSH) ta musanta rahotannin dake yawo kan cewa ta cafke kwamandanta bisa zargin yana da hannu a hare-haren jihar Plateau.
Wasu gungun 'yan bindiga sun kai farmaki kauyen Garam da ke jihar Neja inda suka yi garkuwa da mutum uku. Wannan shi ne karo na biyu da suke kai hari garin.
Labarin Sojojin Najeriya
Samu kari