Zaben jihohi
Shugaban jam’iyyar APC na kasa, ya ji dadin yadda jam’iyyar APC ta lashe zaben Gwamnonin da aka yi a Imo da Kogi, Abdullahi Ganduje ya ya aikawa ‘Yan adawa sako.
Za a ga jerin kananan hukumomin jihar Kogi da ‘Yan takaran da su ka yi nasara a zaben Gwamna. Manyan jam’iyyu hudu su ka tabuka abin a yaba - APC, SDP, PDP da ADC.
An bayyana Ododo na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar Kogi da aka gudanar a jiya Asabar, wanda har yau ake kirga kuri'un.
Hukumar zabe mai zaman kanta, INEC ta ba da umarnin sake zabe a wasu Unguwanni tara da ke karamar hukumar Ogori Magongo da ke jihar Kogi a makon mai zuwa.
Dan takarar gwamna a jam'iyyar PDP, Dino Melaye ya yi martani kan badakalar da ake yi a zaben jihar Kogi, ya kiraye INEC ta soke zabukan da aka yi a wasu wurare.
Yayin da aka sanar da Hope Uzodinma na jam'iyyar APC a matsayin wanda ya lashe zabe, wata 'yar bautar kasa ta bace da na'urar tantancewa da kuma sakamakon zabe.
A zaben Kogi, Sanata Dino Melaye ya rasa karamar hukumar Kabba Bunu, inda ake ganin zai iya kai labari. A shekarar 2007, Dino ya wakilci mutanen yankin a majalisa.
Murtala Yakubu Ajaka ne ya fara samun nasara a kan Ahmad Usman Ododo da Dino Melaye. ‘Dan takaran Jam’iyyar SDP ya ci karamar hukumar da aka fara sanarwa.
Gwamnan jihar Imo, Hope Uzodinma ya lashe dukkanin ƙananan hukumomi 27 a zaɓen gwamnan jihar Imo da aka gudanar a ranar Asabar, 11 ga watan Nuwamban 2023
Zaben jihohi
Samu kari