Zaben jihohi
Yayin da ake shirye-shiryen gudanar da zaɓen fidda gwanin gwamnan jihar Ondo, wasu magoya bayan dan takarar gwamna a jami'yyar APC sun tarwatsa zaɓen.
A ranar Talata ne majalisar dokokin jihar Abia ta zartar da kudirin dakatar da biyan kudaden fansho ga tsofaffin gwamnoni da mataimakansu a jihar.
Duk da cewa babu wata doka a Najeriya da ta hana tsofaffin gwamnoni neman zama sanatoci, amma manazarta na ganin kamar sun mayar da abun al'adar su.
Ga dukkan alamu shugaban majalisar dokokin jihar Ondo, Oladiji zai fuskanci barazanar tsigewa bayan ya ari bakin ƴan majalisa ya ci musu albasa ba da yawunsu ba.
Kakakin majalisar dokokin jihar Bauchi, Babayo Akuyam da mataimakinsa Ahmed Abdullahi sun yi murabus daga mukamansu bayan dawowar Suleiman da Dahiru.
Gwamna Abba Kabir Yusuf na jihar Kano ya mika sunayen ‘yan kwamitin riko 17 na kowace karamar hukumar jihar ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa.
Betty Akeredolu, Matar tsohon gwamnan Ondo, Rotimi Akeredolu ta caccaki surukarta, Funke Akeredolu Aruna bayan ta nuna goyon baya ga Gwamna Lucky Aiyedatiwa.
Ana fatan Isa Pantami ya zama Gwamnan Gombe. Kalubalen farko a gaban malamin shi ne samun tikitin APC, daga nan sai karbuwa a wajen kiristoci da ke Gombe.
Wasu da ake zargin ’yan bangar siyasa ne dauke da makamai sun yi awon gaba da mutane biyar da aka shirya za su ba da shaida a kan zaben gwamnan Kogi.
Zaben jihohi
Samu kari