Zaben jihohi
Kasa da awanni 24 kafin gudanar da zaben fidda gwani a gobe Asabar, dan takarar gwamna a APC, Fasto Osagie Ize-Iyamu ya janye daga takarar gwamnan jihar Edo.
Hukumar zabe ta ƙasa INEC ta ce wasu 'yan daba sun hargiza zaben cike gurbi da jami'an hukumar ke gudanarwa a jihar Enugu, an lalata kayayyakin zabe gaba daya.
Rahotannin da ke shigo mana yanzu na nuni da cewa misalin karfe 1:58 na ranar Laraba aka rantsar da Duoye Diri a karo na biyu a matsayin gwamnan jihar Bayelsa.
Oluwole Oke, dan majalisar wakilai, ya gabatar da kudirin kafa sabbin jihohi uku a shiyyar kudu maso yammacin kasar, sun hada da; Oke-Ogun, Ijebu, da Ife-Ijesa.
Tsohon mamban Majalisar jihar Ondo, Hon. Tomide Akinribido ya watsar da kashin jam’iyyar PDP tare da komawa APC mai mulkin jihar a jiya Juma'a 9 ga watan Faburairu.
Dan takarar gwamna na jam’iyyar NNPP a zaben 2023 a jihar Akwa Ibom, John Akpanudoedehe, ya ce zai iya komawa jam'iyyar APC ne kawai idan aka cika wasu sharudda.
Kakakin majalisar tarayya, Tajudeen Abbas ya rantsar da 12 daga cikin zababbun mambobi 15 da hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC ta gabatar a ranar Laraba.
Majalisar dokokin jihar Osun ta dakatar da shugaban karamar hukumar Ede ta Kudu, Mr. Lukman Afolabi saboda furta kalaman cin mutunci ga kakakin majalisar jihar.
Jam'iyyar APC mai adawa a jihar Delta ta lashe dukkan zabukan kujerun Majalisar jihar da aka gudanar a ranar Asabar 3 ga watan Faburairu a jihar.
Zaben jihohi
Samu kari