Karatun Ilimi
Shugaban ƙasa, Asiwaju Bola Ahmed Tinubu ya amince da samar da motocin Bas a manyan makarantun gaba da sakandire a sassan ƙasar nan domin tallafawa ɗalibai.
Shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu ya gargadi makarantun gaba da sakandare kan karbar kudade ba tare da dalili ba ganin yadda ake cikin matsin tattalin arziki.
Ana kyautata zaton Bola Tinubu zai yi aiki da kwararru wajen gudanar da mulkinsa. Ya zabi wasu manyan sanannun masu ilimi da gogewan da ya kamat ku sani a kai.
Mataimakin shugaban jami'ar Abuja, Farfesa Abdul Rasheed Na'Allah ya ce dole ko wane dalibi ya yi rijista da kamfani kafin kammala digiri don rage rashin aiki.
'Yan sanda sun cafke dalibai su 10 da suka ci zarafin malami bayan ya hana su satar amsa a jarabawa a jihar Ogun, sun tare shi ne bayan an tashi a makaranta.
Gwamnan jihar Enugu, Peter Mbah a ranar Asabar, ya samu digirin digirgir a fannin Dabaru da kere-kere daga makarantar Said Business School na Jami’ar Oxford.
Gwamnatin jihar Kano ta dakatar da shugabannin makarantun sakandare guda uku a jihar saboda rashin kula da aiki da zuwa aiki ba akan lokaci ba da wasu laifuka.
Kungiyar Malaman Kwalejin Ilim a Najeriya ta umarci mambobinta da suke zuwa wurin aiki sau biyu a sati saboda halin da ake ciki a na cire tallafin man fetur.
Hukumar gidajen yarin Najeriya ta ce akalla fursunoni biyar ne suka kammala digiri a gidan gyaran hali na Kuje da ke birnin Tarayya Abuja yayin zamansu a gidan.
Karatun Ilimi
Samu kari