Kannywood
Rahama Sadau ta yi wa Yusuf Lazio sha tara ta arziki da ta gigita shi, inda ya gode mata tare da kiranta 'uwa', kuma ya roƙa mata albarka bisa karamcinta.
Dattijo kuma jarumin Kannywood, Malam Inuwa Ilyasu, ya bayyana cewa ya shiga harkar fim ne domin fadakar da jama'a da kuma koyar da addinin Musulunci.
Hisbah ta hana sauraron wakar Amanata ta Hamisu Breaker, tana ganin tana yada alfasha, amma mutane da dama sun zargi hukumar da tallata wakar, domin ba a santa ba.
Mawakin siyasa, Dauda Kahutu Rarara zai aure jarumar Kannywood, Aisha Humaira a Maiduguri na jihar Borno bayan sun dade suna aiki tare a fagen rara waka da amshi.
Shahararriyar jarumar fina-finan Nollywood, Doris Ogala ta ba da labarin yadda ta mutu, ta je cikin aljanna, amma Ubangiji ya umarce ta da ta dawo duniya.
Bayan rasuwar fitaccen jarumin Kannywood, Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, ya nuna alhinin rasuwar Abdullahi Shuaibu da aka fi sani da Karkuzu a Jos.
Jarumin Kannywood, Malam Abdul Kano da aka fi sani da Baba Karkuzu rasuwa bayan rashin lafiya da ya yi fama da ita. Ali Nuhu ya sanar da rasuwarsa a Filato.
Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya yabi Baban Chinedu da ya fara wa'azin kalubalantar Kiristoci a Najeriya. Asadussunnah yana tare da Baban Chinedu.
Jarumi a masana'antar Kannywood, Sadik Sani Sadik ya ce yana fim ne ba don koyar da tarbiyya ba, illa neman kuɗi kawai saboda tarbiyya daga gida ake samu.
Kannywood
Samu kari