Jihar Kano
Don rage cunkoso, daga jihar Kano ministan cikin gida ya sallami fursuononi 150, yayin da babbar jojin jihar Gombe ta sallami fursunoni 182 daga jihar Gombe.
Jam'iyyar APC ta zargi Gwamna Abba Kabir da kashe makudan kudaden jihar wurin daukar nauyin zanga-zanga a jihar madadin ya jira hukuncin kotu tukunna.
Tsofaffin ma’aikatan da su ka yi ritaya za su je gidan gwamnatin jihar Kano da karfe 9:00 na Asabar dauke da takardunsu domin a tantance su saboda a biya fansho.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya daukaka kara bayan kotun zabe ta tsige shi, ya ba APC nasara wanda shari'ar ta jawo surutu.NJC ta ce za a kafa kwamiti da zai yi bincike.
Alhassan Ado Doguwa, dan majalisa mai wakiltar mazabar tarayya ta Tudun Wada/Doguwa a jihar Kano, ya ce ba yawan kuri'u kadai ke sa a ci zabe ba.
An gurfanar da matar ne mai suna Hafsa bisa zargin ta yi wa mijinta dukan tsiya kan hira da 'yan mata a waya. Kotu ta kulle ta zuwa 11 ga watan Disamba, 2023.
Wani magidanci ya shigar da matarsa aure a gaban kotun shari'ar musulunci da ke Kano bisa zarginta da yin aure bisa aure. Ya nemu kotu ta raba auren.
Shugabannin NNPP sun bukaci ayi adalci a shari’ar zaben Kano ko kuwa rikici ya barke a Afrika, jagorori da magoya bayan NNPP su na cigaba da zanga-zanga da addu’o’i.
Mahaifiyar rikakken dan daba da ake nema ruwa a jallo a jihar Kano, ta yi ta-maza inda ta mika shi ga 'yan sandan jihar a ranar Talata. Ta nemi a yi masa afuwa.
Jihar Kano
Samu kari