Jihar Kano
Babbar Kotun Tarayya ta umarci Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya gurfana a gabanta nan da mako daya don jin bahasi daga gare shi kan karar da aka shigar da shi.
Hukumar Hisbah ta jihar Kano ta cafke wata babbar mota makare da kwalaben barasa fiye da dubu 24 da aka kwace daga hannun masu fasa kwauri da tsakar dare.
Shahararren Gwamna ya jawo Fasto da Inyamuri ya ba su babban mukami Jihar Arewa. A ranar Talata aka ji Abba Kabir Yusuf ya rantsar da karin hadimai.
Gwamnatin jihar Kano za tayi wa duk wani ma’aikaci karin kudi a albashi. Ma’aikata, ‘yan fansho za su samu karin N20, 000 da N15, 000 daga Disamban 2023.
Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin, ya rabawa wasi bayin Allah tallafin motoci kirar sharon guda 60 domin su dogara da kansu a Kano.
Shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya soki jigon jam'iyyar, Salihu Lukman kan kalamansa da zargin ya na shugabanci irin na Abdullahi Adamu.
Gwamna Abba Kabri Yusuf da mai gidansa, Rabiu Kwankwaso sun taya al'ummar Najeriya murnar shiga sabuwar shekara inda suka koka da kalubale a 2023.
Dubunnan mata ne suka yi gangamin nuna goyon baya ga gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf tare da yin addu'o'in samun nasararsa a Kotun Koli kan shari'ar gwamna.
Dan Majalisar Tarayya da ke wakiltar mazabar Fagge ya sha suka a wurin 'yan mazabarsa bayan kaddamar da shirin kaciya ga yara fiye da dubu daya a Kano.
Jihar Kano
Samu kari