Jihar Jigawa
Gwamnan jihar Jigawa, Ahmed Umar Namadi ya kaddamar da shirin rabon kayayyakin tallafi ga mutanen da bala'in ambaliyar ruwa ta ritsa da su a jihar.
An samu asarar rayukan mutum uku bayan wani gini ya rufto a jihar Jigawa. Jami'an 'yan sanda sun yi nasarar ceto mutanen da ginin ya rufto a kansu.
Fasinjoji biyar da wani jirgin ruwa ya ɗauko sun rasa rayuwarsu a lokacin da ya nutse a garin Ganta da ke ƙaramar hukumar Buji a jihar Jigawa jiya Talata.
Rahotanni sun nuna wani mai shayi ya lakaɗawa matashi duka har lahiraa jihar Jigawa kan zarginsa na ɗaukar burodi, madara da indomi, yan sanda sun kama shi.
Gwamnatin tarayya ta ce mamakon ruwan sama da ambaliyar ruwa ya kashe akalla mutane 49 a jihohin Taraba, Adamawa da Jigawa,ana fargabar karuwar ambaliya.
Ministan tsaron Najeriya, Mohammed Badaru, ya ba da tallafin N20m ga gwamnatin jihar Jigawa sakamakon annobar ambaliyar ruwan da ta auku a jihar.
Gwamnatin jihar Jigawa ta ce an fara biyan yan fansho hakkokinsu wadanda su ka ajiye aiki a shekarar da mu ciki wanda adadin kudin ya kai Naira Biliyan 3.4.
Rundunar yan sanda a jihar Jigawa ta tabbatar da mutuwar wata mata mai shekaru 40 bayan cinnawa kanta wuta a jihar saboda sakinta da mijinta ya yi.
Masu zanga zanga a Jigawa sun bukaci gwamna Umar Namadi ya sauke kwamishinan noma na jihar, Muttaka Namadi daga karamar hukumar Ringim kan rashin yin aiki.
Jihar Jigawa
Samu kari