
Gobara







An samu tashin wata mummunar gobara a wata babbar kasuwa da ke birnin Gusau a jihar Zamfara. Gobarar ta lakume shaguna masu yawa a kasuwar ta babura.

Rahotannin da ke shigo mana daga jihar Oyo sun nuna cewa an tafka asarar makudan kuɗi a gobarar da ta tashi a kasuwar sayar da kayan gayarn ababen hawa.

Kamfanin man NNPCL ta tafka asara. Wannan ya biyo bayan tashin gobara ana tsaka da sauke fetur. Duk da jami'an kashe gobara sun isa wurin, wutar ta ci iya cinta.

Gwamna Muhammadu Umaru Bago na jihar Neja ya nuna damuwa kan yawaitar tashin gobara a Minna, ya bukaci hukumomin da lamarin ya shafa su wayar da kan jama'a.

Hukumar kwana-kwana ta jihar Kano ta tabbatar da mutuwar ma'aurata sakamakon wata gobara da ta afku a yankin karamar hukumar Ungogo a jihar Kano.

An samu tashin wata gobara a fitacciyar kasuwar Alaba Rago da ke jihar Legas. Gobarar wacce ta tashi da tsakar dare ta lalata kayayyakin miliyoyin naira.

Wata mata da ba a san ko wacece ba kawo yanzu ta shallake rijiya da baya yayin da wani sindari da aka ajiye a kwalabe ya yi bindiga a jihar Legas

Rahotanni sun bayyana cewa masu shagunan ɗinki a wata kasuwar zamani da ke Lafia, babban birnin jihar Nasarawa sun yi asarar kayan miliyoyin Naira.

Rahotanni sun tabbatar da cewa gobara ta kama a ofishin hukumar NSIPA inda ta yi sanadin lalacewar abubuwa a ma'ajiyar ciki har da kayan horaswa na N-Power.
Gobara
Samu kari