Yan bindiga
An tabbatar da mutuwar dakarun takwas na rundunar yan sanda takwas da aka nema aka rasa bayan arangama da yan bindiga a jihar Benuwai ranar juma'a da ta gabata.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin ta'addanci a jihar Plateau. 'Yan bindigan sun yi garkuwa da wani basarake tare da wasu mata zuwa cikin daji.
Wasu miyagun 'yan bindiga sun kashe Hon. Ejeh Udeh, babban jigon jam’iyyar APC a Otukpo, jihar Benue, bayan sun kai masa hari a gidansa da tsakar dare.
Dan bindiga mai shekara 70 a jihar Katsina, Sani Geza ya nuna farin ciki kan sulhu da aka yi a karamar hukumar Matazu. 'Yan bindiga sun yarda su ajiye makamai.
An bukaci shugaban kasa Bola Tinubu da ya umarci sufeton 'yan sandan Najeriya da a dauki matakan hana 'yan bindiga samun makamai a Najeriya da suke kai hari.
'Yan bindiga sun kashe jami’an ‘yan sanda biyar da wani mutum daya a wurare daban-daban a Abugi da Isanlu, jihar Kogi, tare da kwace bindigoginsu.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun kai harin kwanton bauna kan jami'an tsaro a jihar Benue. Ana fargabar cewa an hallaka sama da jami'ai guda 10.
Rundunar ’yan sanda a Zamfara ta cafke fitaccen jagoran ’yan bindiga Muhammadu Kan Kani, yayin da a Imo da Rivers aka kama mambobin IPOB/ESN guda biyar.
Wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun tafka ta'asa yayin da su ka yi awon gaba da hadimin gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule. Sun sace shi ne a gidansa.
Yan bindiga
Samu kari