Aiki a Najeriya
Hukumar karbar korafe-korafe da yaki da rashawa ta jihar Kano ta bayyana kama wasu ma’aiakatan gwamnati guda biyu kan zargin sayar da takardun aiki ga mazauna jihar.
Shehu Sani ya yi mamakin yadda gwamnan Edo ya gamsu da biyan N70,000 a matsayin mafi karancin albashi amma wasu gwamnoni sun gaza amincewa da hakan.
Bincike ya fallasa yadda gwamnatocin jihohin kasar nan 30 suka kashe makudan kudi wajen sayen kayan kwalam da makulashe da walwalar jami'an zaman gwamnati.
Gwamnatin Gombe za ta kashe naira biliyan 20 kan gina titi mai tsawon kilomita 18.5 a ciki da wajen kwaryar jihar. Kwamishinan ayyuka na jihar ne ya sanar da haka.
Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya bayyana babban titin da gwamnatinsa ke ginawa daga Lagos-zuwa Calabar da alamar ci gaba ce da zai samar da aikin yi.
An kama wasu matasa a jihar Neja bisa zargin sace fankoki a masallaci, inda aka kama wani kuma da laifin datse hannun wani dan acaba da kuma sace babur.
Gwamnatin tarayya za ta kaddamar da tashar tsandauri a Funtua dake jihar Katsina gobe Alhamis, wanda zai zama tasha irinta ta uku a Arewacin Najeriya.
Gwamnatin jihar Kano ta ce ba gaskiya ba ne cewa za ta kori masu sharar da gwamnatin Abdullahi Umar Ganduje ta dauka aiki kamar yadda wasu ke yadawa.
Gwamnatin jihar Kano ta kaddamar da ginin titin dan Agundi mai hawa uku domin rage cunkoson ababen hawa. Kamfanin CCG Nigeria Limited ne zai yi aikin kan ₦15bn.
Aiki a Najeriya
Samu kari