Zaben Najeriya
Shugaban hukumar zabe ta kasa watau INEC mai jiran gado, Farfesa Amupitan ya isa fadar shugaban kasa da ke Abuja domin karbar rantsuwar kama aiki daga Tinubu.
Shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Godswill Akoabio ya bayyana cewa an samu ci gaba da tsarin gudanar da zaben tun bayan kifar da PDP a zaben 2015.
A labarin nan, za a ji cewa tsohon gwamnan jihar Kano, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya yi gargadi mai zafi ga yan siyasa da ke fice wa daga tsarin Kwankwasiyya.
Jagoran jam'iyyar NNPP, Olufemi Ajadi Oguntoyinbo ya yi gargadi kan neman dawo da zaben 2027 zuwa 2026. Ya ce lamarin zai kawo matsaloli da dama a Najeriya.
Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar APC, Dr. Nicholas Felix, ya raba man fetur kyauta ga mazauna karamar hukumar Oredo, Jihar Edo, a ranar Litinin.
Akalla ‘yan takara 14 daga jam’iyyar APC sun bayyana aniyarsu ta kalubalantar Gwamna Ademola Adeleke na PDP a zaben 2026 a Osun. Daga cikin su akwai Otunba Omisore.
Dan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaben 2023, Peter Obi ya karyata jita-jitar da ke yaduwa cewa Atiku Abubakar, na shirin karɓe tikitin a ADC.
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike, ya musanta rahotannin da ke cewa yana shirin neman kujerar shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.
Shugaban majalisar dattawa, Godswill Akpabio, ya yi ikirarin cewa an yi masa magudin zabe a shekarar 2019. Sai dai, an gano cewa ikirarin nasa karya ce.
Zaben Najeriya
Samu kari