Dandalin Kannywood
Allah ya yiwa mahaifiyar marigayi Ahmad S Nuhu rasuwa. Shugaban hukumar fina finan Najeriya, Ali Nuhu ya sanar da lokacin da za a yi mata jana'iza a Jos.
Mawaka irinsu Sadiq Saleh, Ado Gwanja, da Umar M Shareef sun yi fice a 2024 da wakokinsu na soyayya, al'adun Hausa, da kuma salon da ke sanya rawa a gidajen biki.
Ali Nuhu ya gargadi jaruma Rayya kan yunkurin da take yi na zana tattoo. 'Yan Kannywood da dama sun mara masa baya, suna neman ta dakatar da wannan shiri.
Adam Zango ya zargi daraktan Kannywood da cin kudin marayu har N550,000. Daraktan ya ce su hadu kotu yayin da Zee Zango ta goyi bayan ikirarin Zango kan kudin.
Hassan Giggs ya gode wa Hadiza Gabon bisa abubuwan alherin da ta rika yi masa, yana yabawa kaunarta ga iyalinsa da jajircewarta a masana'antar Kannywood.
Mawaki Rarara ya saki sabuwar wakar biki wadda ya yiwa Alhaji Ibrahim Yakubu da amaryarsa, Khadija. Bidiyon wakar ya jawo ce-ce-ku-ce a soshiyal midiya.
Bilkisu Salis, jarumar Kannywood, ta sha suka kan shigar da ta yi a hotunan da ta wallafa a Instagram, yayin da wasu ke yaba kyawunta wasu kuma na aibata ta.
Ado Gwanja ya saki kundin wakoki mai taken Dama Nine wanda ya ƙunshi sababbin wakoki 18, yanzu ana iya sauraron su a YouTube, Audio Mack da Apple Music.
Rayya Kwana Casa’in ta saki hotuna don murnar ranar haihuwarta, sun jawo ce-ce-ku-ce yayin da wasu suka yi fatan alheri, wasu kuma suka nuna rashin jin dadi.
Dandalin Kannywood
Samu kari