Kotun Kostamare
Wani mutumi James Bassey ya durkusa ya na neman alfarma bayan an yanke wa wanda ya ke kara hukunci a kotu, ya ce ya na neman alfarma saboda taimakonsa da ya ke.
Rundunar 'yan sandan jihar Bayelsa ta kama wasu mutane uku da ake zargi sun kashe wani matashi bisa zargin satar biredi a birnin Yenagoa da ke cikin jihar.
An kai lauyan mutum-mutumi na farko gaban kuliya bisa zargin yi wa doka hawan kawara a kasar Amurka. Lauyan mai suna 'DoNotPay' dai na fuskantar zarge-zarge ne.
Rundunar 'yan sandan jihar Kano ta musanta zargin cewa an kashe daya daga cikin jami'anta a jihar yayin artabu da 'yan ta'adda a kasuwar Rimi a ranar Talata.
Wata babbar kotun Abuja ta ba DCP Abba Kyari beli kan naira miliyan 50 a tuhumar da ake yi masa da yan uwansa biyu na kin bayyawa hukumar NDLEA kadarorinsu.
Kotu ta tura wani matashi Auwal Usman gidan gyaran hali, sakamakon samunsa da lafin datsewa abokinsa Sabo Abduwa hannu a yayin da rigima ta kaure tsakaninsu.
Wata kotu da ke zamanta a Dei-Dei a birnin Abuja ta tsare wani matashi mai suna Darlington Chibundu bisa zargin satar jita da makirfo guda biyu a cikin majami'a
Wata kotun majistare da ke jihar Bayelsa ta tsare wani matashi mai suna Kingsley Solomon a gidan kaso bisa zargin satar jaririya mai watanni biyu a duniya.
Hukumar Yaki da Cin Hanci (EFCC) reshen jihar Borno ta gurfanar da wani mai suna Isiyaku Ibrahim da ake zargi da handame dukiyar marayu da ya kai har N12m.
Kotun Kostamare
Samu kari