Dan takara
Lauyan APC a kotun zabe, ana shirin jikawa Peter Obi aiki bayan ya shigar da kara, ya ce tun farko Obi ba 'Dan LP ba ne, kuma bai tsaida abokin takararsa ba.
Wani ‘Dan LP ya ce Peter Obi yana ganin barazana, kamar yadda yake fada, tun da ya tsaya takarar shugabanci a Jam’iyyar LP, ake bin sa da kulle-kullen yakarsa.
APC ta samu kudi masu yawa ta hanyar saida fam din shiga zaben 2023, sai ga shi wani shugaba a APC ya bukaci Abdullahi Adamu ya dawo da wadannan tulin kudi.
A zaben Gwamnonin Jihohin da Hukumar INEC ta shirya, a Zamfara, Kano da Bauchi, sai da Jam’iyyun adawa sai da suka yi da gaske kafin su doke Jam'iyyar APC.
An sake samun Jam’iyyar da ta kalubalanci nasarar Bola Tinubu a kotun zabe. All Peoples Movement ta na ganin Atiku Abubakar ya kamata ya gaji Muhammadu Buhari.
Za a ji Gwamnatin Kano ta yi kira ga zababben gwamnan jihar Injiniya Abba Kabir Yusuf ya yi hakuri, ya daina fitar da sanarwar hukuma da sunan shawara ga jama’a
Abba Kabir Yusuf ya nada kwamitin da zai yi aikin karbar mulki daga hannun Abdullahi Umar Ganduje. Abdullahi Baffa Bichi shi ne shugaban kwamitin na mutum 65.
Gwamnan Zamfara ya ce duk wata rumfar zabe da ke jihar sai da aka baza soja akalla 50 domin a kai jam’iyyarsa ta APC kasa, a karshe Lawal Dauda ya yi galaba.
Zababben Gwamnan jihar Kano a NNPP ya ce iyalinsa ba za su shiga harkar shugabancin jama’a ba. Abba Gida Gida yana so Nasiru Yusuf Gawuna ya dauki kaddara.
Dan takara
Samu kari